Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ajax ta sayi Steven Bergwijn daga Tottenham
Ajax ta sayi dan wasan gaban Tottenham, Steven Bergwijn daga Tottenham kan yuro miliyan 26.
Dan wasan, mai shekara 24, dan kasar Netherland, ya rattaba hannu jan yarjejeniyar shekara biyar.
Bergwijn ya ci wa Tottenham kwallo 8 a wasanni 81 da ya yi bayan zuwa daga PSV Eindhoven a Janairun 2020.
"Hakan ya nuna karara cewa Steven ya zabi ya koma taka leda a Ajax", cewar kociyan kungiyar Alfred Schreuder.
"Kwararren dan wasa ne da yake da hazaka. Burinsa shine samun nasarori a duk inda yake, ina cike da farinciki cewa mun yi nasarar sayo shi," in ji Alfred.
Kudin da Ajax din ta sayi Steven ya kasance masu yawa da kuma ya shiga sahun wadanda aka fi saya da tsada a kungiyar.