Ten Hag ya ji daɗin rashin tafiyar Maguire

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Erik ten Hag ya ce ya yi farin ciki da Harry Maguire ya ci gaba da zama a Manchester United - kuma a yanzu dole ne mai tsaron bayan ya yi yaki domin dawo da matsayinsa a kungiyar.

Maguire - wanda aka fara da shi a wasan firimiya takwas kacal a kakar wasan data gabata - ya shirya komawa West Ham amma cinikin na fam miliyan 30 ya warware.

Dan wasan bayan na Ingila, mai shekara 30, yana son sake buga wasa akai-akai, kuma kocin United Ten Hag ya ce ya kamata ya yi yunkuri amfani da duk damar da zai samu.

Maguire, wanda ya yi fama da rashin buga wasanni sosai a kakar da ta gabata, an cire shi daga mukamin kyaftin ɗin kungiyar a watan Yuli. Ya rike mukamin tun watan Janairun 2020.

Ya kasance dan wasa da ba a yi amfani da shi ba a nasarar da United ta yi a kan Wolves a gasar Premier ranar Litinin.