Man City ta kammala sayan Mateo Kovacic daga Chelsea

An wallafa

Manchester City ta kammala ɗaukar dan wasan tsakiya na Croatia Mateo Kovacic daga Chelsea kan kuɗi fan miliyan 25.

Cinikin ɗan shekara 29 na da fan miliyan biyar a gefe na tsarabe-tsarabe, ya kuma sanya hannu ne kan kwantaragin shekara huɗu.

Kovacic shi ne ɗan wasan farko da City ta saya a wannan kakar tun bayan kofuna uku da ta ci, Chamipions da Premier da FA.

"Wannan mataki ne mai kyau a wajena, yanzu kawai jira nake naga randa zan fara taka leda a City," in ji Kovacic.

Ya zo ne lokacin da ɗan wasan ƙungiyar ɗan Jamus Ilkay Gondogan ya koma Barcelona bayan da kwantaraginsa ta ƙare da City.

A gefe guda kuma ta yi tayin fan miliyan 90 ga ɗan wasan tsakiya na Ingila, tayin da ƙungiyarsa West Ham United ta yi watsi da shi.

Ya ƙara da cewa: "Duk mai kallon wannan ƙungiyar ƙarƙashin kocinta Pep ya san ƙungiya ce mai kyau - su ne ƙungiyar da suka fi kowacce kyau a duniya. Kofunan da suka ci za su tabbatar da maganata, sune kulob din da ya fi kyau a yanzu.

"Zai iya zama burin duk wani ɗan kwallo a duniya taka leda a City. Ina da abubuwa da zan koya domin bunƙasa kaina, na kuma yi amannar cewa ƙarƙashinPep zai ƙara zama kwararran ɗan kwallo, wanda hakan abin alfahari ne.

"Shirina na yanzu shi ne na samu na huta na wasu makonni kafin na dawo Manchester domin tunkarar kaka mai zuwa. Ina son taimakawa kulob ɗin ya ci gaba da zama na ɗaya ya kuma ci gaba da cin kofuna."

Ya koma Chelsea ne daga Real Mardid a watan Agustan 2018, a matsayin aro, kafin daga baya kuma a saye shi kan kwantaragin shekara 5.

Ya bugawa ƙungiyar wasa 37 a bara da ta kammala a matsayi na 12, kakar da tana ɗaya daga cikin marasa daɗi da ta taɓa yi a tarihi.

Kovacic na cikin tawagar Chelsea da ta ci Champions a 2021, ya shiga a matsayin sauyi a wasan da suka yi nasara kan City da ci 1-0