Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham taƙi amincewa da tayin da Man City ta yi mata kan Declan Rice £90m
West Ham United taƙi amince da tayin da Manchester City ta yi mata na fan miliyan 90 kan kyaftin ɗinta Declan Rice.
Tayin da City ta yi ya haɗa da ainihin kuɗin sayan dan wasan fan miliyan 80 wanda ya yi ƙasa da fan miliyan 100 da West Ham ke nema.
Ana tsammanin Arsenal za ta yi tayi na uku kan ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 24.
Tayi na biyu da Arsenal ta yi na fan miliyan 75 ta ce za ta biya huɗu ne, da ƙarin fan miliyan 15 na wasu tsarabe-tsarabe, wanda West Ham ɗin ta ƙi amince da shi a makon jiya.
Kwantaragin Rice a West Ham za ta ƙare ne a 2024, ko da yake akwai zaɓin ƙarin shekara guda a yarjejeniyarta zuwa 2025.
Tun bayan nasarar da ƙungiyar ta samu na lashe kofin Europa Conference League kan Fiorentina a farkon wannan watan, shugaban ƙungiyar David Sullivan ya ce yana da tabbacin ɗan wasan zai bar ƙungiyar a wannan kakar.
Duk da cewa suna tattaunawa kan ɗan wasan Chelsea na tsakiya Mateo Kovacic kan kuɗi fan miliyan 25, kuma ga tafiyar Ilkay Gundogan zuwa Barcelona, Pep Guardiola ya matsu ya ɗauki ɗan wasan domin ƙara ƙarafafa tsakiyarsa da kwararrun 'yan wasa.