Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli wasu daga cikin sabbin rigunan ƙungiyoyin Premier na bana
Ƙungiyoyi da dama na Premier Ingila sun fara nuna sabbin rigunan da za su rika sanyawa a gida a gasar 2023 da 2024.
Cikin waɗanda suka nuna sabbin rigunan har da gwarzuwar gasar Premier Manchester City, wadda ta lashe kofina uku a bana.
A dai Manchester, makobciyar City wato abokiyar hamayyarta Manchester United ta tallata tata rigar da za ta riƙa sakawa a wannan shekarar a wasannin gida.
Idan muka kaɗa arewacin Landan Tottenham Hostpur itama ta bayyana tata inda wasu daga cikin 'yan wasanda maza da mata suka sanya rigunan a jikinsu.
Arsenal da ta riƙe teburin Premier na tsawon watanni, kuma daga baya ta gaza kai wa ga nasara ita ma ta cire tata rigar gwanin sha'awa