An yi canjaras a damben ɗan Aliyu da Autan na Aisha a Maraba

Ɗan Aliyu da Autan na Aisha sun yi damben turmi uku ba kisa a wasan ranar Lahadi da safe a gidan Idris Ɓamɓarewa da ke jihar Nasarawa, Najeriya.
Tun a makon da ya gabata aka sa ladan naira 100,000 a dambe tsakanin ɗan wasan Arewa da na Guramaɗa.
A ranar Lahadi sai da Laraban ɗan Gwamba mawakin 'yan dambe ya fara yi wa ɗan Aliyu kiɗa daga baya ya yi wa Autan na Aisha.
Magoya bayan 'yan damben biyu sun yi ta yi musu alheri tun kan su taka damben a tsakaninsu da kowa ke son ganin yadda za ta kaya.
Bayan da aka natsu ne alkalin wasa Anas ya kama hannun 'yan damben biyu ya ɗaga sama da cewar sune za su guɗa dambe a lokacin.
Daga nan ne suka fara wasa, kuma tun ba a yi nisa ba ɗan Aliyu ya dunga kai dambe, inda Autan na Aisha shi ma ya tayar da na sa kwazon.
Turmi na biyu kuwa 'yan wasan biyu sun yi ƙoƙari sosai, amma ɗan Aliyu ne ke kai dambe, Autan na Aisha ya yi ta kewaye-kewaye, amma yana kai bugu.
Daga nan suka je shan ruwa, inda Idris Ɓamɓarewa ya buƙaci su koma turmi na uku, sai dai turmi na uku bai kayatar ba kamar na farko da na biyu.
Wasu wasannin da aka buga a ranar ta Lahadi:
Shagon Dogon Messi ya buge Mabilu.
Autan Autan ɗan Bunza ya buge Shagon Rabe.
Jan idon Guramaɗa ya yi nasara a kan Shagon Ɗandigiri
Jan idon Guramaɗa ya buge Shagon Mustapha.
Sai rabe Shagon Ebola da ya doke Ɗan Bichi.
Karawar da aka yi canjaras a gidan Ɓambanɓarewa:
Basiru da Ɗan Bichi
Shagon na Aisha da Inda
Dogon Inda da Shagon Bahagon Ali Yaro











