Arsenal ta shirya ƙalubalantar Man City a kakar wasan bana - Arteta

Asalin hoton, Getty Images
Mikel Arteta ya ce ƴan wasan Arsenal sun shaida masa cewa suna buƙatar samun ci gaba a kakar wasa ta bana yayin da suke neman taka wa Manchester City birki a yunkurinta na kare kambun da ta lashe a kakar da ta gabata, wanda hakan zai zama karo na biyar a jere.
Gunners ta ƙare a matsayi na biyu a kaka biyu na gasar firmiya da suka gabata, kuma ta ƙare ne da maki biyu kacal a bayan ƙungiyar Pep Guardiola a kakar wasan da ta wuce.
Bayan wasan ƙarshe na kakar wasan da ta gabata da Everton, Arteta da ƴan wasansa sun gudanar da wani taro a tsakiyar birnin Landan wanda ya samu halartar shugaban ƙungiyar Josh Kroenke, da ma'aikatan kulob ɗin.
Arteta ya ce "Duk ƴan wasan sun shaida mun, 'za mu yi ƙoƙari, mun san za mu iya, dole mu sami ci gaba."
"Su ne ke jagorantar wannan buri."
Arsenal za ta kara da Wolves a filin wasa na Emirates a wasansu na farko a gasar wannan kakar a ranar Asabar, kuma Arteta ya ce ƙungiyarsa a shirye ta ke, ta fara yaƙin neman lashe kambun gasar.






