Willian da Fulham sun yi hannun riga

Willian

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Willian ya tabbatar da cewa zai bar Fulham bayan shekaru biyu yana taka leda a kulob ɗin

Ɗan wasan mai shekara 36, ​​ya koma ƙungiyar ne a watan Satumba na shekarar 2022 bayan ya bar ƙungiyar Corinthians ta Brazil, inda ya fara sana'ar sa.

Willian ya tabbatar da cewa ya bar Fulham a wani dogon bayani a shafinsa na Instagram, bayan ya bugawa kulob ɗin wasanni 67, ya kuma ci ƙwallo 10.

Willian ya shafe shekaru 10 yana taka leda a gasar firimiya, kuma duk a ƙungiyoyin da ke birnin Landan.

Ya shafe shekara bakwai tare da Chelsea tsakanin 2013 zuwa 2020, inda ya lashe kofunan Firimiya biyu, da kofin FA da kuma Europa League.

Willian ya shafe shekara guda a Arsenal bayan ya bar Chelsea kafin ya koma Brazil inda ya bugawa Corinthians a shekara ta 2021.