Newcastle ta shiga zawarcin Bryan Mbeumo, Arsenal na bibiyar Leroy Sane

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle United na fatan ɗaukar ɗan wasan gaban Brentford da Kamaru mai shekara 25, Bryan Mbeumo, a watan Janairu. (Telegraph - subscription required)

Liverpool da Arsenal ma su na bibiyar Mbeumo, wanda Brentford ta yi wa kuɗi £50m. (Newcastle Chronicle)

Manchester United na fatan gaggauta naɗa kocin Sporting, Ruben Amorim a matsayin sabon mai horas da ƴan wasanta kafin wasan gasar firimiya da za ta buga da Chelsea a filin Old Trafford a ranar Lahadi. (Times - subscription required)

Sai dai Manchester United na fuskantar ƙalubalai game da wa'adin da za ta bayar kafin Sporting ta sakar mata Amorim, wanda ya kai makonni. (Mail)

Amorim zai jagoranci Sporting a wasan da za ta buga ranar Juma'a, kafin zuwansa Manchester. (CNN Portugal)

Ɗan ƙasar Portugal ɗin mai shekara 39 ya na fatan ɗaukar ɗan wasan bayan Sporting Goncalo Inacio mai shekara 23 da ɗan wasan gaban Ingila, Marcus Edwards mai shekara 25, da kuma ɗan wasan gaban Portuguese forward Pedro Goncalves, mai shekara 26, Da zarar ya koma Manchester United.(Teamtalk)

Ana sa ran kocin Manchester united na riƙon ƙwarya zai bar ƙungiyar idan aka naɗa Amorim (Independent)

Manchester City ta na fatan Pep Guardiola zai tsawaita zamansa kocin ƙungiyar nan ba da jimawa ba. (Mail), external

Manchester United na sha'awar ɗaukar aɗan wasan bayan Canada, Alphonso Davies, amma ɗan wasan na shirirn komawa taka leda a Real Madrid.

Arsenal ta na ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan Jamus, Leroy Sane, mai shekara 28, idan kwangilarsa ta ƙare a Bayern Munich.(Football Insider)