Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ci tarar Chelsea da Nottingham Forest kan hatsaniyar ƴan wasa
An ci Chelsea tarar fam 40,000 yayin da Nottingham Forest za ta biya fam 125,000 saboda rikicin da ya kaure tsakanin ƴan wasansu a lokacin da ƙungiyoyin biyu suka fafata a gasar Firimiya a farkon wannan watan na Oktoba.
Ƙungiyoyin biyu sun amsa laifin tuhumar da hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta masu bayan lamarin da ya faru a ƙarshen wasan da suka tashi 1-1 a Stamford Bridge ranar 6 ga watan Oktoba.
Ɗan wasan baya na Forest Neco Williams ne ya tayar da hayaniyar a lokacin da ya tunkuɗe ɗan wasan baya na Chelsea Marc Cucurella shi kuma ya ci karo da kocin Blues Enzo Maresca, wanda hakan ya haifar da hatsaniya a wajen fili.
Hukumar gudanarwa da ke zaman kanta ta bayyana cewa ƙungiyoyin biyu sun amsa laifinsu amma ta ce hukuncin ya kamata ya nuna cewa abin da ya faru mummunan lamari ne da ya shafi ƴan wasa masu yawa daga ɓangarorin biyu.
Tarar Forest ta fi yawa saboda wannan shi ne karo na shida da irin wannan lamari ya shafi ƙungiyar a cikin kaka uku da suka gabata, yayin da shi ne karo na uku da ya shafi Chelsea a cikin shekaru biyar.
Hukumar ta ce rashin nadama da Forest ta nuna na ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya hukuncin ya yai tsanani, inda ta ƙara da cewa babu wata shaida cewa kulob ɗin na yunƙurin magance abin da ya zame mata babbar matsala a yanzu.