Arteta zai iya komawa Man United - Rio Ferdinand

Asalin hoton, getty images
Arteta ya taka muhimmiyar rawa a ci gaban da Arsenal ke samu tun lokacin da ya karɓi aiki a Emirates a watan Disamban 2019.
Amma da wannan muhimmin ƙoƙarin da yake yi a arewacin Landan, tsohon ɗan wasan Machester United Rio Ferdinand ya yi iƙirarin cewa Arteta ba zai yi jinkiri ba idan ya samu damar zama kocin United.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai Ferdinand ya ce: ''Dari bisa ɗari, Arteta zai iya barin Arsenal ya koma United. Zai iya.''
Ya ƙara da cewa "Babu wanda ke cewa hakan na faruwa amma idan Man United ta wayi gari ta ce, 'Erik ten Hag, mun gode', ko kuma Erik ten Hag ya tafi Bayern Munich...Kuma United ta ce: 'Arteta ne kan gaba a jerin sunayen mu', zai ce wa ƴan wasansa 'ku yi hakuri amma, zan tafi, Allah Ya ba da sa'a a kakar wasa ta gaba'.
Arsenal dai tana taka rawar gani a farkon shekarar 2024, inda ta zura ƙwallaye 25 a dukkan wasannin da ta buga, kuma ta samu nasarar lashe wasanni shida na gasar Premier a jere a yunƙurinta na lashe gasar Premier League ta bana.
A halin yanzu dai babu wasu raɗe-raɗin cewa Arteta yana da niyyar barin Arsenal.







