Messi zai ja ragamar Argentina wasa da Australia da Indonesia

Asalin hoton, Getty Images
Argentina za ta buga wasan sada zumunta da Australia a Beijing da kuma Indonesia a Jakarta kamar yadda hukumar kwallon kafar kasar ta sanar.
Kyaftin, Lionel Messi ne zai ja ragamar wasan da za a buga da Australia ranar 15 ga watan Yuni a Workers Stadium.
Wasan zai zama maimaici ga wanda suka fafata a tsakaninsu a gasar kofin duniya a Qatar a zangon 'yan 16.
Argentina ce ta ci karawar da 2-1, kuma Messi ya zura kwallo a raga a fafatawar a gasar da suka lashe kofin karo na uku jimilla.
Haka kuma Argentina za ta buga daya wasan sada zumunta da Indonesia ranar 19 ga watan Yuni a Jakarta.
Shugaban hukumar kwallon kafar Australia, James Johnson ya ce wasan da za su buga a Beijing, zai karfafa hulda tsakaninsu da China.
Kusan shekara 15 rabon da Australia ta buga wasa a kasar China, bayan da dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu.
Yanzu dai abubuwa sun fara komawa daidai a China, bayan da kasar ta yi fama da barazanar cutar korona.









