Bayani a sauƙaƙe kan bashin da ke neman kai Amurka ƙasa

Asalin hoton, Getty Images
Da farko dai, kokarin kayyade Iyakar bashin da Amurka za ta iya ci dambarwa ce ta siyasa.
An kirkiro shi ne domin samun madogara wajen zartar da wani kudiron doka da nufin ceto kasar daga mummunan tabarbarewar tattalin arziki.
Menene haƙiƙanin abin da ke faruwa a nan?
Gaskiyar zance, gwamnatin Amurka tana kashe kuɗin da suka zarce wadanda ta ke samu, saboda haka, tana bukatar cin bashi domin tafiyara da harkokinta.
Kuma akwai iyakar bashin da za ta iya ciyo wa. Gashi dai ta na bukatar karin kudi, kuma wajibi ne sai majalisa ta amince.
A baya dai wannan abu ne da ya zama ruwan dare, amma yanzu abubuwa sun canza.
Yan jam’iyyar Republican suna ganin wannan a matsayin wata dama da za su iya amfani da ita wajen cimma muradunsu, kamar rage yawan tallafin da ake bayar wa a bangaren samar da muhalli ko kuma rage kudaden tallafin da ake baiwa masu karamin karfi.
Sai dai kuma shugaban Amurka Joe Biden ya hau kujerar naki, inda ya ce sai dai majalisar ta zartar da wannan kudirin doka ba tare da neman cimma wata ,manufa ta daban ba.
Amma fa lokaci na ƙurewa
Akwai yiyuwar gwamnatin Amurka ta fadi kangin rashin kudi daga ranar Daya ga watan Yuni.
Me wannan mataki zai iya haifarwa?
Da farko dai, ma’aikatan gwamnati ba za su sami albashi ba.
Su ma masu cin gajiyar shirin tallafa wa masu karamin karfi ba zasu samu kudin da suka saba samu ba.
Harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi za su durkushe, kuma dubban mutane za su rasa ayyukansu.
Amma babban illar da wannan shiri zai haifar itace jefa masu zuba jari cikin yanayin rashin yarda da karfin kasar a fannin biyan bashin da ke kanta.
Irin wannan bashi yana zuwa ne a matsayin wani tallafi daga baitulmalin gwamnati, wanda ake yiwa kallon Daya daga cikin bangarori mafi kwanciyar hankali ga masu sha’awar zuba jari.
Kuma hakan zai gaggauta dusashe yarda da duniya ta yi da Amurka.











