Raƙuma da rawar bikin gargajiya na Samburu a Kenya cikin hotunan Afirka

An wallafa

Wannan maƙala na ɗauke da zaɓaɓɓu kuma ƙayatattun hotunan Afirka na makon 6 zuwa 12 ga watan Oktoban 2023.

.

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP

Bayanan hoto, Kwana ɗaya bayan zaɓe a Liberia wani mutum na rera waƙoƙin addini a Cocin Monrovia babban birnin ƙasar.
.

Asalin hoton, GUY PETERSON/AFP

Bayanan hoto, Ƴan wasan ƙwallon ƙafa yayin da suke buga ƙwallo ranar Juma'a a birnin Clara da ke Monrovia na Liberiya.
.

Asalin hoton, GERALD ANDERSON/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Juma'ar dai, al'ummar yankin Samburu ne da ke Kenya suke rawa a lokacin da suke bikin al'adun gargajiya.
.

Asalin hoton, GERALD ANDERSON/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Jama'a sun yi dandazo yayin bikin na Maralal International a ranar Asabar.
.

Asalin hoton, MATTHEW LEWIS/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Masu Gasar Tseren Raƙuma lokacin tseren kilomita 10 yayin da ƴan yawon bude ido daga ƙasashen ƙetare suke kallo.
.

Asalin hoton, BILLEL BENSALEM/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, On the same day, a chef shows off a special technique at the International Couscous Festival in Algeria's capital, Algiers.
.

Asalin hoton, AMANUEL SILESHI/AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi al'ummar Oromo da ke ƙasar Habasha na bukin Irreecha wanda suke gudanarwa kowacce shekara.
.

Asalin hoton, AMANUEL SILESHI/AFP

Bayanan hoto, Mutane sanye da kayan gargajiya sun taru don ibada a tafkin da ke Hora Arsadi kusa da birnin Bishoftu a yankin Oromia.
.

Asalin hoton, AMANUEL SILESHI/AFP

Bayanan hoto, Yayin bukin al'adun gargajiya na Irreecha, mahalarta sun watsa ciyawa cikin tafkin bayan sun zuba ruwan a jikinsu da nufin kawo karshen lokacin damuna.
.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Wani mutum a birnin Afirika ta Kudu na wucewa ta kusa da zanen jan hankali don zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.