Wane mataki kuma magoya bayan Peter Obi za su ɗauka?

.

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Wasu daga cikin matasan da suka fara zaɓe a karo na farko a Najeriya sun ji ba daɗi bayan da wanda suke goyon baya ya zo na uku a zaɓen shugaban Najeriya da ya gudana ranar 25 ga watan Fabarairu.

An ba su shawara kada hakan ya karya masu gwiwa, domin kuwa nasara na nan gaba.

Wannan ya biyo bayan zaɓukan jihohi da aka jinkirta gudanarwa a wannan wata, bayan ɗaga zaben gwamna da na ‘yan majalisu da aka yi ana saura kwana uku.

Gwamnatin jiha ce ke gina makarantu da asibitoci da titunan cikin gari da kula da harkokin sufuri da sauransu waɗannan duka ayyukanta ne.

Wasu matasa da suka nuna sha’awarsu a siyasa suka kuma goyi bayan ɗan takarar jam’iyyar Labour sun karaya da abin da ya faru a ranar zaɓe.

A wasu yankuna: kamar sace akwatun zaɓe, da tayar da rikici da rashin zuwan jami’an zaɓe a kan lokaci abin da ya hana wasu da yawa yin zaɓen.

Wanda wannan ka iya zama dalilan da suka sa bai samu kaso mai yawa ba ke nan inda ya ƙare da kashi 27 cikin ɗari.

Amma shugaban yaƙin neman zaɓen jam’iyyar Rinu Oduala ya ce Obi da magoya bayansa sun kama suna a ƙasar bai kamata su sare ba.

“Ba a samun sauyi a dare ɗaya. Yana faruwa ne mataki-mataki. Lokaci zuwa Lokaci.

Kuma mun tunkari kawo sauyi kan goben ƙasarmu,” in ji wani magoyin bayan LP.

.

Masu sanya ido sun soki yadda aka gudanar da zaɓen saboda ya gaza kai yadda suka yi tsammani, yayin da jam’iyyar PDP da LP suka ƙalubalanci zaɓen a kotu.

Magoya bayan Obi irinsu Oduala sun nuna farin cikinsu da yadda jam’iyyar ta cimma gagarumar nasara cikin wata tara tun bayan da Obi ya fito takarar shugabancin Najeriya.

Ya samu ƙuri’a miliyan shida – kashi 25 cikin 100, wanda wannan ba ƙaramin ƙoƙari ba ne idan aka yi la’akari da irin yadda jam’iyya mai mulki APC da kuma PDP da ta kawar da mulkin soja a 1999 suka yi kaka-gida a harkokin siyasar ƙasar.

Yanzu jam’iyyar Labour na da kujerar sanata 109, ta kuma samu kujera 35 cikin 360 na ‘yan majalisun wakilai.

Wannan nasarar ta nuna cewa ƙarfin ikon da ake da shi a siyasance yana hannun mutane.

Yadda fafatawar za ta kasance a jiha mafi arziƙi

.

Asalin hoton, AFP

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan jiya Mista Obi ya kayar da jam’iyya mai mulki a Jihar Legas, duk da cewa an samu rahoton tsaiko da rikici kan zaɓen.

Da alama gwamnan yanzu da ke kan mulki Babajide Sanwo-Olu ya tsorata da sakamakon zaɓen, domin kuwa ya riƙa aikewa da sakonnin Twitter yana nuna wa magoya bayansa irin nasarorin da ya yi a ofis.

Yana neman wa’adi na biyu amma yaƙi amincewa ya yi mahawara da sauran ‘yan takara, kamar na Labour Gbadebo Rhodes-Vivour.

Gwamnan za a iya cewa ya yi ƙoƙari yadda ya kamata a shekara huɗun da ta gabata.

Ya ƙaddamar da titin dogo da aka kwashe gwamman shekaru ana yi, ya kuma tafiyar da lamarin annobar korona kamar yadda ya kamata.

A wajen wasu, abin da ya faru a ranar 20 ga watan Oktoba 2020, lokacin da sojoji suka buɗe wa masu zanga-zangar EndSars, wuta suka kashe aƙalla mutum tara, abu ne mai wuyar mantuwa.

“Sun kashe wuta sun kashe kyamara sannan suka buɗe mana wuta,” in ji Adeola Owosho wani da ya tsallake rijiya da baya.

Nasarar da aka samu a Legas za ta bai wa magoya bayan Obi ƙwarin gwiwar samun nasara a zaɓen gwamnoni mai zuwa.

Ƙona katin zaɓe

.

Asalin hoton, BBC/GIFT UFUOMA

“Na yi zaɓe a cikin ruwa da fatan za a sanya ƙuri’ata, amma gaskiya ba a yi ba, “ in ji Naya Benson a Abuja, inda masu zaɓe da yawa suka yi zaɓen cikin yanayi maras kyau.

Wasu sun yi fushi sosai ta yadda suka riƙa ƙona katin zaɓen nasu suna cewa sun raba gari da siyasa

“Na ƙona katina saboda na fuskanci abin duk ɓata lokaci ne,” haka wani mai zaɓe ya shaida wa BBC.

Ya kafa hujja da cewa INEC ta gaza ɗora sakamakon zaɓe a shafinta kan lokaci kamar yadda ta yi alƙawari.

INEC ta nemi afuwa kan jinkirin da aka samu, tana cewa cunkoson da aka samu na intanet ne ya haifar da hakan.

Ko ba komai ‘yan Najeriya sun gano lagon yadda manyan jam’iyyu suka yi kaka gida a siyasar ƙasar, sai dai abin tambayar a nan shi ne, an ya matasan za su iya jurewa wannan fafutuka?