Za mu yi karo-karon kuɗi domin tsawaita zaman Antony a Betis- Isco

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan tsakiya na ƙungiyar Real Betis, Isco ya ce idan ya kama ƙungiyar za ta yi karo-karon kuɗi domin tsawaita zaman aron ɗanwasan ƙungiyar Manchester United, Antony.
Antony ɗan ƙasar Brazil ya zura ƙwallo huɗu, sannan ya taimaka an ci ƙwallo huɗu a wasa 12 da ya buga tun bayan zuwansa aro da zai zauna zuwa ƙarshen kakar bana.
Wata majiya daga Manchester United ta ce Betis ce take biyan kusan kashi 84 na albashin Antony na fam 100,000 a mako.
"Za mu yi karo-karo domin mu tsawaita zamansa aƙalla zuwa wata shekarar," in ji Isco a tattaunawarsa da DAZN.
"Mun ga canji tun lokacin da ya iso. Yana taimaka masa sosai. Ina farin cikin zuwansa wannan ƙungiya. Ya ba mu mamakin yadda yake da sauƙin kai da burin sadaukar da kansa ga ƙungiyar."
Tun bayan zuwan Antony Betis, wasa biyu ne kawai ƙungiyar ba ta ci ba a cikin wasa 12, sannan doke Sevilla da ta yi ne na nasara ta shida a jere a gasar La Liga.
Yanzu Betis ce ta shida a teburi, kuma ƙungiyoyi huɗu ne ke zuwa gasar cin kofin gasar Champions League daga Spain.
Antony ya koma Manchester United ne daga Ajax a shekarar 2022 kan fam miliyan 81, wanda shi ne mafi tsada bayan Paul Pogba a ƙungiyar.
Ya zura ƙwallo 12 a wasa 96 a zamansa da United, amma ƙwallo ɗaya kawai ya ci a gasar Premier tun daga watan Afrilun 2023.
A kakar bana ya buga wasa 13 cikin wasa 33 na United kafin ya tafi zuwa Betis.
Ita kuma Betis ɗanwasan da ta saya da ya fi tsada shi ne Denilson wanda ta tsaya a fam miliyan 22 a shekarar 1998.









