Barcelona na bibiyar Victor Osimhen, ƙungiyoyin Turai na rubibin Etta Eyong

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City da Manchester United da kuma Arsenal na rubibin sayen ɗan wasan gaban Kamaru mai shekara 22 da ke taka leda a Levante, Karl Etta Eyong, wanda ke neman sanin makomarsa a watan Janairu. Barcelona da Real Madrid ma suna son ɗan wasan. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Manchester United ba ta zawarcin ɗan wasan AIK, Kevin Filling, duk da rahotannin da ke cewa ƙungiyar ta fara tattaunawa kan sayen ɗan wasan gaban Sweden ɗin mai shekara 16. (Manchester Evening News)

AC Milan za ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke neman ɗan wasan gaban Manchester United mai shekara 24, Joshua Zirkzee, idan har ɗan ƙasar Netherlands ɗin zai sauya sheƙa a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Zakarun Jamus Bayern Munich na tattaunawa da ɗan wasan bayan Feyenoord da Netherlands mai shekara 19, Givairo Read, wanda ƙungiyoyin gasar Firimiya ciki harda Liverpool ke neman sa. (Sky Sports - in German)

Da wuya tsohon kocin Tottenham da Nottingham Forest Ange Postecoglou ya zamo kocin Celtic, inda hankali ya karkata ga kocin Ipswich Town Kieran McKenna da kuma na Wales, Craig Bellamy. (Sky Sports)

Har yanzu Barcelona na bibiyar ɗan wasan gaban Galatasaray Victor Osimhen, mai shekara 26, amma farashin da aka sanya wa ɗan wasan Najeriyan na janyo koma baya. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Chelsea ta shige gaba a ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban Juventus Kenan Yildiz, bayan gabatar da tayi mai gwaɓi kan ɗan wasan Turkiyyan mai shekara 20. Amma Arsenal da Manchester United da kuma Liverpool na sha'awar ɗan wasan. (Teamtalk)

Ɗan wasan bayan Barcelona Eric Garcia ya amince da sabuwar kwangila da ƙungiyar duk da cewa akwai ƙungiyoyi irin Chelsea da Tottenham da ke zawarcin ɗan wasan Sifaniyan mai shekara 24. (TBR Football)

Tottenham na fatan ɗauko ɗan wasan gaban Juventus da Canada, Jonathan David a watan Janairu, yayin da Bayern Munich ke bibiyar ɗan wasan mai shekara 25.(Fichajes - in Spanish)