Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Vinicius Junior ya nemi afuwar masoya ƙungiyar kan abin da ya aikata a lokacin da aka sauya shi a wasan hamayya tsakanin Madrid da Barcelona a ranar Lahadi.
An cire Vinicius ne daga wasa a minti na 72, inda a maimakon ya koma kan kujerar ƴanwasa sai ya zarce ɗakin sauya kaya domin nuna rashin jin daɗi da matakin.
Daga baya Vinicius ya fito ya koma kan benci a wasan, wanda Madrid ta yin nasara da ci 2-1, sannan bayan hura tashi daga wasa ya shiga cikin ƴanwasan da suka ƙalubalanci ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Vinicius ya ce: "A yau na nemi afuwar dukkanin Madridistas saboda abin da na aikata a lokacin da aka sauya ni a wasan Clasico".
Ya ƙara da cewa "ina kuma son na nemi afuwar abokan wasana da ƙungiyar da kuma shugabanta.
"Wani lokaci shauƙi yakan rinjaye ni kasancewar a kodayaushe nakan so na yi nasara kuma na taimaki ƙungiyata.
"Ƙoƙarina na ganin na yi gogayya ya samo asali ne daga ƙaunar da nake yi wa wannan ƙungiya da duk wani abu da ya jiɓance ta".
Real Madrid ta ɗauki
Vinicius ne daga ƙungiyar Flamengo a shekarar 2018 kan kudi fam miliyan 38.7,
kuma tun daga lokacin ya ci wa Madrid ƙwallaye 111 a karawa 335.
Sai dai babu
tabbas kan ci gaba da zaman matashin a Madrid, inda rahotannin baya-bayan nan
ke nuna cewa ƙungiyar a shirye take ta sayar da ɗan wasan idan suka samu tayi
mai gwaɓi.
A cikin sanarwar
neman afuwa da ya fitar, Vinicius bai ambaci sunan mai horaswa Xabi Alonso kai tsaye ba a
cikin waɗanda ya bai wa haƙuri, yayin da ake ci gaba da raɗe-radin cewa mutanen
biyu ba sa ga-maciji.