Gavi ya koma kan ganiya a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Barcelona, Gavi ya koma kan ganiya a wasannin da yake buga wa a kakar nan tun bayan da ya kammala jinya.
Ya sake koma fagen fama a bana daga ranar 20 ga watan Oktoba a wasan da Barcelona ta doke Sevilla 5-1 a La Liga.
Bayan sama da kwana 348 da ya sha jinya, yanzu yayi kwana 89 da komawa buga wa Barcelona tamaula, wadda kawo yanzu ya yi mata karawa 17 a dukkan fafatawa.
Tun bayan da ya koma taka leda daga jinya, Magoya bayan ƙungiyar sun ci gaba da goyon bayan ɗan wasan da yi masa tafi a duk lokacin da ya yi bajinta.
Cikin wasa 17 da ya yi wa Barcelona kawo yanzu, ya ci ƙwallo biyu ya kuma bayar da biyu aka zura a raga.
Shi ne ya fara cin ƙwallo a Spanish Super Cup zagayen daf da karshe da Athletic, sannan ya bai wa Lamine Yamal wadda ya zura a raga.
Haka kuma a wasan karshe da Real Madrid a Sifanish Super Cup, shi ne Camavinga ya yi wa keta da Barcelona ta samu fenariti, inda Lewandowski ya buga ya ci.
Haka kuma Gavi ya ci ƙwallo a wasan da Barcelona ta doke Betis 5-1 ranar Laraba a Copa del Rey zagayen ƴan 16, ya kuma taka rawar gani sosai.











