Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na farautar Antony, Man United kuwa tana zawarcin Lorenzo Lucca
An bayyana ɗanwasan Brazil Antony mai shekara 25, a matsayin wanda Arsenal ke zawarcinsa yayin da ɗanwasan mai buga wa Manchester United ke taka rawar gani a zaman aron da yake a Real Betis. (Fichajes - in Spanish)
Manchester United na ƙyalla ido kan ɗanwasan Udinese Lorenzo Lucca, 24, a kasuwar cefanar da ƴanwasa ta lokacin bazara. (Sun - subscription required)
Tottenham na fatan kaucewa rasa ɗanwasan Sweden Dejan Kulusevski, 24, a wannan bazarar yayin da AC Milan da Napoli suke zawarcinsa. (GiveMeSport)
Dole Arsenal ta sa Nico Williams mai buga wa Sifaniya wasa ya zama ɗaya daga cikin ƴanwasanta masu daraja idan tana son ta ɗauko shi daga Athletic Bilbao a wannan bazarar. (Telegraph - subscription required)
Bayer Leverkusen ta tuntuɓi wakilan Stefan Ortega mai shekara 32 kuma tana iya ɗaukan golan na Manchester City a kan euro miliyan takwas. (Bild - in German, subscription required)
Tauraruwar ɗanwasan Deportivo La Coruna Yeremay Hernandez, mai shekara 22, na haskawa a wurin Arsenal da Chelsea. (Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford, 27, zai yi la'akari da rage albashinsa idan yana son ya koma Aston Villa a matsayin dindindin daga Manchester United a wannan bazarar. (Football Insider)
Kusan ƴanwasan Arsenal 11 har da ɗanwasan Ukraine Oleksandr Zinchenko, 28, da ɗanwasan Poland Jakub Kiwior, 25 na iya barin ƙungiyar a bazara domin haɓaka ƙarfin ƙungiyar wajen sayen ƴanwasa a kasuwar musayar ƴan ƙwallo. (Mirror)
Lecicester City na ƙyalla ido kan kocin Sheffield Wednesday Danny Rohl idan Ruud van Nistelrooy ɗan asalin Netherlands ya bar ƙungiyar a bazara. (Mail)
Aston Villa na farautar ɗanwasan Real Madrid mai shekara 20, Arda Guler bayan da Liverpool ta daina nuna sha'awarta kan ɗanwasan na Turkiyya. (Teamtalk)
Ɗanwasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 19, na nan kan ƙudirinsa na zuwa Manchester United, duk da yadda Real Madrid da Inter Milan ke zawarcinsa (GiveMeSport)