Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Lewandowski
Barcelona ta cimma yarjejeniya da Bayern Munich, domin dauko dan wasan gaba na kasar Poland, Robert Lewandowski, a cewar Herbert Hainer, shugaban kungiyar.
Dan wasan mai shekara 33, wanda saura kaka daya kwantiraginsa ta kare a kungiyar Jamus, ya fada mata cewa yana son ya tafi.
Lewandowski ya ci wa Bayern kwallo 50 a cikin wasa 46 a kakar Bundesliga da aka kammala.
Ya kuma taimaka mata lashe babban kofin gasar Jamus karo 10 a jere.
"Abu ne mai kyau wajen samun daidaito daga kowane bangare " in ji shugaban kungiyar.
"Mun cimma yarjejeniyar da Barcelona .
"Robert kwararren dan wasa ne, kuma ya ci dukkan kofuna tare da mu. Mun jinjina masa matuka ."
Lewandowski ya koma Bayern daga Borussia Dortmund a 2014, sannan ya ci kwallo 344 a cikin wasa 374 a kungiyar, wanda hakan ya sanya shi a mataki na biyu cikin wadanda suka fi zurawa kungiyar kwallaye a tarihi bayan Gerd Muller.
Dan wasan, dan kasar Poland ya ci kofin Bundesliga a dukkan kakar wasanni 8 da ya yi a Bayern, wanda ya taimaka mata lashe gasar Zakarun Turai a 2019-20.