An raba maki tsakanin Arsenal da Chelsea a Stamford Bridge

Asalin hoton, Getty Images
An tashi 1-1 tsakanin Chelsea da Arsenal a wasan mako na 11 a Premier League da suka fafata ranar Lahadi a Stamfor Bridge.
Ƙungiyoyin biyu sun tashi ba ci a mintin 45 ɗin farko, bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka zura ƙwallayen a raga.
Arsenal ce ta fara cin ƙwalllo ta hannun Gabriel Martinelli, yayin da Chelsea ta farke minti 10 tsakani ta hannun Pedro Neto.
Da wannan sakamakon Chelsea ta ci gaba da zama a mataki na uku da maki 19 iri ɗaya da na Arsenal ta huɗun teburi.
Nottingham Forest tana ta biyar da maki 19, kamar yadda Brighton take da 19 a mataki na shida a teburi, bayan kammala wasan mako na 11.
Ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba, Chelsea za ta je King Power domin fafatawa da Leicester City a karawar mako na 12.
Haka kuma ƙungiyar ta Stamford Bridge za ta je Heidenheim ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba a Europa Conference League.
Arsenal kuwa za ta karɓi bakuncin Nottingham Forrest a wasan mako na 12 ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba.
Daga nan Gunners za ta je Sporting ranar Talata 26 ga watan Nuwamba a Champions League.
Abinda ya kamata ku sani tsakanin ƙungiyoyin:
Wasa ɗaya Chelsea ta ci Arsenal daga haɗuwa 11 a baya a dukkan fafatawa, shi ne 2-0 da ta yi nasara a Premier a Emirates a Agustan 2021, inda aka doke ta karawa bakwai da canajaras uku.
Chelsea ta kasa cin wasa daga shida da ta fuskanci Arsenal a gida, wadda ta yi canjaras uku da Gunners, sannan ta yi rashin nasara uku.
Wasan da suka buga a bara a Premier League:
Premier League Talata 23 ga watan Afirilun 2024
- Arsenal 5 - 0 Chelsea
Premier League Asabar 21 ga watan Oktoban 2023
- Chelsea 2 - 2 Arsenal











