Bayern Munich na son Varane, Chelsea ta samu koma-baya a cinikin Moscardo

Raphael Varane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Raphael Varane
An wallafa

Chelsea a shirye take ta yi watsi da zawarcin da Fulham ke yi wa ɗan wasa mai kai hari na ƙasar Albania, Armando Broja, mai shekara 22 a watan Janairu. (Evening Standard)

Arsenal za ta bar mai tsaron ragar Ingila, Aaron Ramsdale ya tafi a ƙarshen kakar wasa ta bana, amma dai ɗan wasan mai shekara 25 ba zai tafi a lokacin hada-hadar 'yan wasa ta watan Janairu ba . (90min)

Ɗan wasan tsakiya na ƙasar Holland Donny van de Beek, mai shekara 26, ya ce zai bar Manchester United a watan Janairu, idan ba a ƙara yawan wasannin da yake bugawa ƙungiyar ba, ya kuma bayyana cewa komawarsa Real Sociedad da bazara, ba za ta yiwu ba. (Diario AS, via Sky Sports)

Manchester United na fatan ƙarfafa ɓangarori guda huɗu na kulob ɗin a watan Janairu, ciki har da matakan tsaron tsakiya, inda ake nuna damuwa kan ƙoƙarin ɗan ƙwallon tsakiya na ƙasar Morocco mai shekara 27, Sofyan Amrabat ya zuwa yanzu. (Guardian)

Ɗan wasan bayan Faransa Raphael Varane mai shekara 30, da ɗan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount, mai shekara 24, na cikin yan wasan Manchester United da ke cikin hatsarin waɗanda kulob ɗin zai iya maye gurbinsu. (Guardian, via Express)

Bayern Munich sun gudanar da tattauna a kan yiwuwar sayen Varane daga Manchester United, amma dai suna ganin da wuya a cimma matsaya . (Sky Germany )

Tottenham na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Blackburn Rovers ɗan ƙasar Ingila, Adam Wharton, mai shekara 19. (90min)

Ɗan wasan gaban Ukraine da ke taka leda a Chelsea Mykhailo Mudryk, ɗan shekara 22, na son kulob ɗinsa ya sayo tsohon abokin ƙwallonsa na Shakhtar Donetsk wanda suka fito ƙasa ɗaya, Georgiy Sudakov, mai shekara 21, a lokacin hada-hadar 'yan ƙwallo ta watan Janairu, saboda haɗa 'yan wasan gaban biyu, ƙawance ne mai ƙarfi idan suna buga wa ƙasarsu Ukraine wasa tare. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɗan wasan gaban Ingila, rukunin 'yan ƙasa da shekara 17, Mason Cotcher na yin atisaye da manyan 'yan wasan Arsenal, bayan ya baro Sunderland amma Gunners ɗin na fuskantar gasa daga Rangers wajen sayen ɗan ƙwallon mai shekara 17. (Telegraph)

Manchester United na zawarcin golan Lazio mai shekara 29, Ivan Provedel sai dai kulob ɗinsa ya ce zai iya sayar sayar da shi ne kawai a kan fam miliyan 30. (Il Messaggero, via Football Italia)

Ɗan wasan gaban Jamus mai shekara 27, Timo Werner, ya shirya ci gaba da zama ya ƙwaci hannu a kulob ɗin RB Leipzig, maimakon tafiya Manchester United a watan Janairu. (Metro)

Chelsea ba ta cimma matsaya da Corinthians a kan ɗan wasan tsakiya mai shekara 18, Gabriel Moscardo ba, kuma babu yiwuwar tafiyar ɗan ƙwallon na ƙasar Brazil. (Fabrizio Romano)

Paris St-Germain da wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Firimiya na zawarcin Moscardo, amma Corinthians ta ƙi sallama shi a kan tayin fam miliyan 26. (ESPN)

Dan wasan gefe na Borussia Dortmund Donyell Malen, mai shekara 24, kawo yanzu yana ci gaba da jan hankalin Liverpool, inda kocin kulob ɗin Jurgen Klopp ya kasance babban mai sha'awar sayo ɗan wasan na Holland. (Bild, via Teamtalk)

Arsenal na tunanin sayo ɗan wasan gaba na ƙasar Slovenia mai buga wa RB Leipzig, Benjamin Sesko, mai shekara 20. (Football Transfers)

Real Betis ba ta fidda da rai ba a ƙoƙarin shawo kan ɗan wasan tsakiyar Argentina Guido Rodriguez, mai shekara 29, ya yi watsi da niyyar tafiya Manchester United ko Barcelona, maimakon haka zai ci gaba da taka leda a Seville. (Marca)