Lewandowski da Raphinha ne kan gaba a cin ƙwallaye a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Sabon koci, Hansi Flick ya ɗora Barcelona kan turbar cin ƙwallaye da yawa a bana, wadda kawo yanzu ta zura 22 a wasa shida a La Liga da fara kakar nan.
Babu wata ƙungiya a manyan gasar Turai a kakar nan da ta kai ƙwazon Barcelona a cin ƙwallaye da yawa a bana.
Haka kuma ƴan wasan Barcelona biyu wato Robert Lewandowski da Rahinha ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Lewandowski mai shida jimilla ya ci Villareal biyu a ranar Lahadi da Barcelona ta yi nasara 5-1 a wasan mako na shida a La Liga.
Tun farko ya fara da zura biyu a gidan Valenci a wasan farko da buɗe kakar bana a karawar da suka yi a Mestalla.
Ɗan kasar Poland bai samu ya zura ƙwallo ba a ragar kungiya biyu a bana, wato Rayo Vallecano, inda VAR ta soke ƙwallon da ya ci.
Haka kuma bai samu ya ci Girona ba a ranar da ya buga wa Barcelona karawa ta 100 tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Bayern Munich.
Shi kuwa Raphinha biyar ya ci kawo yanzu, kaka mafi ƙyau da yake bugawa a Barcelona.
Ya ci Valladolid uku rigis, sannan ya jefa biyu a ragar Villareal a karawar da Barcelona ta doke ta 5-1 a wasan mako na shida a La Liga ranar Lahadi.
Kyalin Mbappe na Real Madrid yana da hudu a raga iri daya da na Ayoze Perez na Villareal
Ranar Laraba, Barcelona za ta karɓi bakuncin Getafe a wasan mako na bakwai a La Liga, sannan ta ziyarci Osasuna ranar Asabar a karawar mako na takwas ranar Asabar.











