Manyan tambayoyin da shugaban Senegal ya ki amsawa a jawabinsa

Macky Sall

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Al'ummar Senegal sun kalli jawabin shugaban kasar a gidan talabijin, cike da fatan samun amsar wasu tambayoyi da ke kai kawo a zukatansu bayan dage zaben shugaban kasar
    • Marubuci, Hamet Fall Diagne
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afrique
  • An wallafa

Shugaban Senegal Macky Sall ya yi wa al'ummar kasar jawabi ranar Alhamis kai-tsaye ta gidan talabijin, makonni bayan sanar da matakin dage zaben shugaban kasar wanda aka tsara gudanarwa ranar 25 ga watan Fabarairu.

Matakin jinkirta zaben ya jefa kasar cikin jerin zanga-zanga da ba a taba gani ba cikin shekara 10, tare da haifar da tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar mutum hudu.

"A ranar 2 ga watan Afirilu, 2024, wa'adina a shugaban kasar Senegal zai zo karshe...na fadi wannan magana ne don kawo karshen tababar da ake yi game da haka," in ji Shugaba Sall a jawabinsa na farko lokacin da ya bayyana a talabijin.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yanjarida, ya mayar da hankali kan batun neman yafiya da sasanci a kasar, inda ya tabo batun kudurin afuwa da yake niyyar aika wa majalisar dokokin kasar.

Yaushe za a gudanar da zaben shugaban kasa a Senegal?

Har yanzu babu tabbas kan ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa a Senegal, duk da jawabin baya-bayan nan da Shugaba Macky Sall ya yi wa kasar.

Watakila sai bayan babban taron kasa da majalisar shari'ar kasar ta amince da gudanarwa tsakanin kungiyoyin fararen hula da jam'iyyun siyasa da 'yan-takara da ake shirin farawa a farkon mako mai zuwa.

Shugaba Sall, wanda ya tabbatar da cewa zai sauka daga mulki a ranar 2 ga watan Afirilu lokacin da wa'adinsa zai kare - bai fayyace amsar da al'umar kasar ke muradin ji daga wajenshi ba.

Ya ce ba ya tunanin za a iya yin zaben kafin ya sauka, ya kuma kawar da duk wani tunani na cewa zai yi murabus kafin karewar wa'adinsa.

Da farko shugaban kasar ya ce ya dage zaben ne zuwa watan Disamba, don bayar da dama a magance matsalolin cancantar tsayawar 'yan takara.

To sai dai kotun tsarin mulkin kasar ta ce dage zaben ya saba wa kundin tsarin mulki, don haka ta bayar da umarnin gaggauta gudanar da zaben.

Me zai faru ranar 2 ga watan Afirilu idan ba a zabi sabon shugaban kasa ba?

Yayin da wa'adin Sall zai zo karshe ranar 2 ga watan Afirilu, kuma babu takamaimai magajinsa, ana ci gaba da zama na rashin tabbas game da wanda zai jagoranci kasar idan ya sauka.

Shugaban kasar ya tabbatar wa 'yan Senegal cewa ba za a samu gibin shugabanci ba yana mai cewa ''ba za mu bar kasar ba tare da shugaba ba, hakan ba zai yiwuwa ba.''

“Kundin tsarin mulki ya tanadi maganin kowace irin matsala da za ta taso,” in ji shi.

Sashe na 36 na kundin tsarin mulkin kasar ya yi tanadin cewa : ''Zababben shugaban Senegal zai fara aiki ne bayan hukumar zaben kasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zabe, da kuma karewar wa'adin magabacinsa. Sannan zai ci gaba da aiki har sai an rantsar da sabon shugaban kasa''.

Shin za a saki Ousmane Sonko da Bassirou Diomaye Faye?

A protester holds up a sign bearing the image of Ousmane Sonko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jagoran hamayyar kasar Ousmane Sonko ya shafe kusan wata bakwai yana tsare a gidan yari
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaba Sall ya nuna aniyar sakinsu, amma hakan ya dogara ne kan yadda shari'a za ta kasance.

“Ba zan saba wa shari'a ba. Kasar nake kallo. Ba mutum ba.

Shin Akwai yiwuwar sakin Ousmane Sonko da Diomaye? ''E hakan zai iya yiwuwa. Ya dogara ga lauyoyinsu, da fannin shari'a,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai lokacin da suka tambaye shi.

A kwanakin baya-bayan nan an saki mutum 344 da aka tsare sakamakon zanga-zangar da ta barke a kasar tsakanin watan Maris din 2021 da Yunin 2023.

Sakin nasu na zuwa ne bayan kiraye-kirayen zaman lafiya da kwanciyar hankali da shugaban kasar ya rika yi bayan barkewar zanga-zanga kan matakinsa na dage zaben shugaban kasar.

A ranar 28 ga watan Yulin 2023 ne aka kama Ousmane Sonko, daga nan ne kuma ake ci gaba da tsare shi har kusan wata bakwai.

An zarge shi da aikata laifuka da suka hada da sace wayar wata jami'ar tsaro.

Shi kuwa Bassirou Diomaye Faye hukumar binciken manyan laifukan kasar ce ta kama shi ranar 14 ga watan Afirilun 2023, bayan ya wallafa wani sako a shafin Facebook da a ciki yake zargin wasu alkalan kasar.

A lokacin da yake tsare an tuhume shi da laifuka uku, da suka hada da bata-suna da yin watsi da hukuncin kotu da kuma yunkurin kawo hargitsi.

Bassirou Diomaye Faye shi ne dan takarar shugaban kasar Senegal na farko da zai yi takarar daga gidan yari idan har ba a sake shi ba kafin zabe.

A baya-bayan nan ne Ousmane Sonko ya mara masa baya a takarar tasa, inda ya yi kira ga magoya bayansa da su kada wa Faye kuri'a.