Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Bayern Munich ta sanar cewar tsohon dan kwallon Liverpool, Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia.
Dan wasan tawagar Senegal, ya ci kwallo 12 a karawa 38 da ya yi wa kungiyar Jamus, wadda ta lashe Bundesliga a kakar da ta wuce.
Babban jami'in Bayern, Jan-Christian Dreesen ya ce dan kwallon mai shekara 31 ya ci karo da kalubale tun bayan da ya koma Jamus daga Anfield.
Mane zai koma taka leda tare da Cristiano Ronaldo a Al-Nassr kan fam miliyan 35 kamar yadda ake hasashe.
Irin kudin da Bayern Munich ta dauki Mane a bara kenan daga kungiyar da ke Anfield.
Al-Nassr ta dauki Ronaldo a Disamba, sannan ta dauki dan wasan Croatia, Marcelo Brozovic da na Brazil, Alex Telles da na Ivory Coast, Seko Fofana.





