Hikayata 2022: Labarin 'Garar Biki'

An wallafa

Labarin 'Garar Biki' wanda Amira Souley da ke birnin Maradi a jamhuriyar Nijar ta rubuta shi ne ya zama zakara a gasar rubutun gajerun kagaggun labarai ta Hikayata ta 2022.

Labarin ya yi tsokaci ne kan al'adar gara a kasar Hausa wadda ta zama wani abun gori idan har ba a yi wa amarya ba.

Hakan ne ya jefa ita tauraruwar labarin cikin hadarin aikewa da hotunanta na tsiraici ga saurayinta bisa kudi kalilan duk da manufar ta samu kudin gara.

Daga wannan makon har zuwa 19 ga watan Fabrairun 2023 za mu rinka kawo muku labaran da suka ciri tuta a gasar ta Hikayata.