Shin Onana na cikin matsalolin Manchester United?

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Manchester United na ci gaba da nuna farin cikinsu da nasarar da suka samu a wasan Europa bayan Rasmus Hojlund ya cece su daga haɗarin Viktoria Plzen, amma barazanar ta ta'allaƙa ne da kuskure da golansu Andre Onana ya yi.
Yayin da ake wasan babu ci, a ƙoƙariunsa na yi wa Matthijs de Ligt ya yi kuskure ɗan wasan gaban Plzen Pavel Sulc ya kwace kwallon ya bai wa Matej Vydra ya ci.
Hojlund ya ci kwallo biyu da ta sa aka manta da kuskuren mai tsaron ragar, suka cece United ta koma cin kungiyoyi takwas ɗin farko a teburi.
Amma wannan kuskuren shi ne na biyu cikin wasanni da dama, hakan ya janyo damuwa musamman da za su fafata da abkona hamayyarsu Manchester City a ranar Lahadi.
Ko da yake bayan kammala wasan kyaftin Bruno ya fito yana kare abokin wasansa game da kuskuren da ya yi.
"Ba za a ce Onana ya yi kuskure ba, saboda idan an samu matsala mu ba ma ɗora ta kan mutum ɗaya," kamar yadda ya shaida wa TNT.
"Muna yarda da shi. Ya san ya yi kuskure kuma shi mutum ne mai wayo, yana taimaka mana a wasanni da dama mun amince da kware warsa.
"Muskure wani ɓangare ne na kwallo. Idan har ba za a yi su ba, to ba za a ci kwallo ba kenan. Mun yi ƙoƙari mun nuna kwarewa mun farke, kuma nasara ta zo a ƙarshe.
Waɗanne kurakurai Onana ya yi?
Babu shakka Onana na cikin gololi masu kyau a Premier a bana, ya yi wasannin da ba a zira masa kwallo ba sama da kowa.
Amma wani ɓangare na kuskurensa shi ne, duk lokacin da ya yi sai abin ya zama abin magana.
A bara, ya yi kurakurai biyu da suka kai ga cin kwallo a wasan da Manchester United ta yi 3-3 da Galatasaray, kuskuren ya lalata shirinsu na samaun damar kai wa zagaye na 'yan 16 a gasar Chamapions.
A yanzu kuma ya yi wannan kuskuren na wasan Plzen bayan wanda ya tafka a wasan Nottingham Forest a Premier.
A wannan wasan an yaudare shi ne da kwallon da Morgan Gibbs-White ya buga inda ya yi dama ita kuma ta yi tsakiya.
Forest ta yi nasara a wasan da 3-2, Tsohon ɗan wasan United Phil Jones ya ce ya kamata Onana ya ƙara ƙoƙari.
"Ban ji dadin kallon wasan haka ba, abin babu dadi," in ji Jones.
"Ya kamata ya cire ɗaya daga cikin kwallayen. Yana yawan kuskure, amma dai yana cikin gololi masu kyau a wannan kakar."
Gololin suka fi yawan wasannin da ba a zira musu kwallo ba a 2024-25

Asalin hoton, BBC Sport











