Haaland ya ci ƙwallo uku rigis a wasa karo na 10 a Man City

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta doke Ipswich Town 4-1 a wasan mako na biyu a Premier League ranar Asabar a Etihad.

Ipswich Town ce ta fara cin mai rike da kofin Premier League ta hannun sabon ɗan wasan da ta ɗauka a bana, Sammie Szmodics.

Erling Haaland ne ya ci wa City kwallo uku rigis a wasan, sannan Kevin de Bruyne ya zura ɗaya a raga.

Wannan shi ne karo na 10 da Haaland ya ci ƙwallo uku rigis a wasa a Manchester City, kuma na 23 tun daga lokacin da ya fara taka leda a tarihi.

Haaland wanda ya lashe takalmin zinare a Premier League a bara ya ci kwallo uku a wasa karo shida a City a 2022/23 da kuma uku a 2023/24 da ɗaya a bana.

Magoya bayan Manchester City sun yi ta yi wa Ilkay Gundogan tafi, bayan da aka saka shi a wasan, wanda ya sake komawa City daga Barcelona ranar Juma'a.

Gundogan ya koma Barcelona kan fara kakar bara, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a City, ƙungiyar Sifaniya ta ce zai iya zuwa neman gwada sa'a a wani wurin a watan nan.

City ta sa Gundogan ya maye gurbin Savinho, yayin da Jack Grealish ya canji Jeremy Doku.

Ranar Lahadi City ta je ta doke Chelsea 2-0 a wasan makon farko a Premier League a Stamford Bridge.

Ranar Asabar 31 ga watan Agusta, City za ta je gidan West Ham a karawar mako na uku a Premier League.