Magoya bayan Man United za su saka bakaƙen kaya ranar Lahadi

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An bukaci magoya bayan Manchester United su saka bakaƙen kaya, domin zanga-zanga ga iyalan Glazer kan yadda ƙungiyar ke tabarɓarewa.

United za ta karɓi bakuncin Arsenal a wasan mako na 29 a Premier League da za su kara ranar Lahadi a Old Trafford.

Ƙungiyar da Ruben Amorim ke jan ragama tana ta 14 a teburin Premier League da maki 33, bayan cin wasa tara da canjaras shida aka doke ta karawa 12.

Ƙungiyar magoya bayan mai mabiya da yawa suna adawa da nuna fushinsu tun bayan da iyalan Glazer suka mallaki ƙungiyar a 2005.

Saboda haka magoya bayan sun bukaci a kawo karshen mallakar da iyalan Glazer suka yi wa United, shi ya sa suka bukaci a saka bakaƙen kaya ranar Lahadi.

Sun kara da cewar hakan nuna fushinsu ne kan yadda United take kara lalacewa, sakamakon dunbin bashi da rashin iya gudanar da shugabanci da cin amanar mabiya.

An yi wata karamar zanza-zanga da magoyan bayan United suka gudanar ranar Lahadi a wasan da aka fitar da United daga FA Cup a karawa da Fulham a bugun fenariti.

Magoya bayan Fulham sun mara baya a zanga-zangar da ta hada da kan karin kuɗin tikitin kallon wasa da ɗaga ƙyalle lokacin da ƴan wasa za su shiga fili.

United ta yi waje daga FA Cup na kakar nan, wadda ita take rike da shi, sannan tana ta 14 a kasan teburin Premier League.

Ranar Alhamis, United za ta je Real Sociedad a wasan farko zagayen ƴan 16 a Europa League, kofin da take fatan ɗauka a kakar nan.

United ta yi hasarar sama da £300million a kaka uku baya, wadda a makon jiy ta sanar za ta kara rage ma'aikata 200, tun farko ta kori 250.