Muhawarar ƴan Najeriya kan yi wa ASUU kishiya

An wallafa

A ranar Talata ne gwamnatin Najeriya ta yi wa ƙungiyar malaman jami'a ta ASUU kishiya da sabuwa mai suna Congress of Nigerian University Academics (CONUA) rijista, abin da ya jawo martani iri-iri daga ƙwararru da ma 'yan ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bai wa National Association of Medical and Dental Academics (NAMDA) shaidar rijista, duka da zummar rage wa ASUU ƙarfin iko, kamar yadda masu sharhi ke cewa.

Mista Ngige ya ce ƙungiyoyin za su ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ASUU a jami'o'in ƙasar.

Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne yayin da kotu ta ba da umarnin a sasanta rikicin a wajen kotun gwamnati ta kai ƙarar ASUU gaban kotun ɗa'ar ma'aikata.

Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya zargi malaman jami'a da cin hanci da yin lalata da ɗalibai don ba su makin jarrabawa.

ASUU ta fara yajin aiki tun daga watan Fabarirun shekarar nan ta 2022 tana neman ƙarin albashi da kuɗaɗen farfaɗo da jami'o'i da kuma alawus-alawus.

Shahararren lauya mai gwagwarmayar kare haƙƙi, Femi Falana, ya ce rijistar da aka yi wa ƙungiyoyin ta saɓa wa doka.

A cewarsa, "dokar ƙwadago ta Najeriya ba ta ba da damar yi wa ƙungiya sama da ɗaya rijista a sashe ɗaya ba".

Ministan ƙwadago ne yake ƙara lalata lamarin - Farfesa Jega

Minista Ngige ya ce matakin yi wa ƙungiyoyin rajista yana kan dokar ƙwadago ta duniya, sannan kuma ta fara bin hanyoyin soke rajistar abokiyar rigimar tasu - ASUU.

Martanin da ya biyo bayan wannan yunƙuri sun haɗa da zargin gwamnati da ministan ƙwadago da yunƙurin ƙara zafafa wutar rikici tsakaninta da ASUU, wadda ta ce ba ta damu da kishiyoyin da aka yi mata.

Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta INEC wanda malamin jami'a ne, Farfesa Attahiru Jega ya zargi ministan da mayar da rajin jituwar na ƙashin kansa.

"Ministan ƙwadago na ƙara rura wutar rikicin, ya mayar da rikicin tsakaninsa da ministan ilimi a gefe guda, da kuma tsakaninsa da ƙungiyar ASUU," a cewarsa ta kafar talabijin ta Arise TV.

Ya ci gaba da cewa: "Yayin da mutane da dama ke neman hanyar sasanta rikicin saboda ɗalibai su koma azuzuwansu su ma ASUU su koma aiki, shi (Ngige) kuma na ta faman haifar da matsaloli, har ma ya kai su kotu."

Jega ya ƙara da cewa ƙirƙiro sabbin ƙungiyoyin "zai ƙara yawan matsaloli ne kawai maimakon gyara su".

'Ƙirƙirar sabuwar ƙungiya ba zai taimaki kowa ba'

'Yan Najeriya da dama na ganin ƙirƙirar sabbin ƙungiyoyin yunƙuri ne da bai zama dole ba.

"Dole ne sai ka fahimci yadda ƙungiyoyin ƙwadago ke aiki a ɓangaren ilimi kafin ka gane cewa ƙirƙirar CONUA ba zai taimaka ba," a cewar wani mai suna Abdul Mahmud a shafinsa na Twitter.

Shi kuma wani mai suna Bamidele cewa ya yi: "Idan har aka yi nasarar soke ASUU kuma rajistar CONUA ta ɗore, to ilimi a Najeriya ya mutu a Najeriya."

Shi kuwa Idris Nasidi Zango bayyana farin cikinsa ya yi da matakin yana mai cewa "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Wannan mataki da gwamnati ta dauka ya yi min dadi," kamar yadda ya wallafa a Facebook.

Yi wa sabbin ƙungiyoyin jami'a rijista ko a jikinmu - ASUU

Kungiyar malaman jai'o'i ta kasa ASUU ta ce yi wa sabbin kungiyoyin kwadago rijista da gwamnati ta yi don malaman jami'a wata shiririta ce kawai, kuma hakan ba zai taba zama barazana ga kungiyar ba.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da jaridar Vanguard dangane da yi wa sabbin kungiyoyin rijista.

"Ba abin da ya dame mu. Mu kungiya ce mai ɗa'a da alƙibla kuma mun san abin da muke yi da kuma abin da muke nema. Suna iya bai wa ɗumbin kungiyoyi rijista idan suna so," in ji shi.

"A ganinmu babu wani tasiri da hakan zai yi, kuma ba ma jin wata barazana. Kasar Allah tana da faɗi."