Waiwaye: Lalacewar layin lantarki da yajin aikin likitoci a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Likitoci sun fara yajin aiki a faɗin Najeriya

Likitoci

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwararewa ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwana biyar daga ranar Juma'a, bisa ga matsayar da aka cimma a majalisar zartarwar ƙungiyar.

Ƙungiyar ta bukaci dukkan mambobinta a cibiyoyi daban-daban su bi wannan umarni ba tare da kaucewa ba.

A cewar kungiyar, matakin yajin aikin ya zama dole ne domin matsa lamba ga gwamnati kan buƙatunsu na inganta walwala da kyautata yanayin aiki, tare da tabbatar da ingantacciyar tsarin kiwon lafiya ga 'yan Najeriya.

Sun ce makasudin yajin ba wai cutar da al'umma ba ne, sai dai domin tabbatar da nagartar harkar lafiya a kasa.

Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15

Shugabannin Ansaru

Asalin hoton, ONSA

A ranar Alhamis ne wata babba kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta yanke wa Mahmud Usman, ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

Mutumin wanda hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar a ranar Alhamis ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ya ba shi damar mallakar makamai da aikata ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane.

Alƙalin kotun mai shari'a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ajiye Mahmud Usman a ofishin hukumar DSS har zuwa lokacin da za a kammal shari'a kan sauran zarge-zargen da ake masa guda 31.

A lokacin gabatar da ƙarar, an tuhumi Mahmud Usman da Abubakar Abba da aikata ta'addanci a 2022, ta hanyar kai hari kan barikin soji ta Wawa da ke Ka'inji a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Niger, lamain da ya yi sanadiyar kisan mutane da dama.

Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da buƙatar Natasha ta komawa aiki

NATASHA/AKPABIO

Asalin hoton, Nigerian Senate/X

Majalisar dattawa ta Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, inda ta ce har yanzu ba a kammala shari'ar dakatar da ita ba.

Natasha ta rubuta wasiƙa ne a ranar 8 ga Agustan bana, inda a ciki ta sanar da majalisar shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, inda ta ce wa'adin wata shida da aka dakatar da ita ya cika.

Ta ce kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yuln da ya gabata cewa dakatarwar da aka mata ba daidai ba ne, sannan ta umarci majalisar ta mayar da ita bakin aiki.

El-Rufa'i ya shigar da ƙorafi kan zargin ƴansanda da cin zarafi

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai

Asalin hoton, NASir El-Rufai/Facebook

A cikin makon da ya gabatan ne tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i, ya shigar da ƙorafi ga hukumar kula da ƴansanda kan zargin ƴansandan jihar da cin zarafi.

El-Rufai ya ce cin zarafin ya haɗa da aikata rashin ƙwarewa da amfani da muƙami ba bisa ka'ida ba, da kuma saɓa wa dokar Ƴansanda ta 2020 da ƙa'idojinta.

Wannan ƙorafi, wanda mai magana da yawu El-Rufa'i, Muyiwa Adekeye, ya fitar a shafinsa na X, ya nuna buƙatar gudanar da bincike mai zaman kansa kuma cikin gaskiya.

A cikin sanarwar, El-Rufa'i ya ce "ina shigar da wannan ƙorafin ne a matsayin ɗan ƙasa mai kishin ƙasa da kuma tsohon jami'in gwamnati da ya yi hidima a matakai na tarayya da na jiha.

NUPENG ta jingine yajin aiki bayan tattaunawa da matatar Dangote

Motocin mai

Asalin hoton, NNPCL/X

A ranar Litinin ne ƙungiyar ta fara yajin aiki domin nuna damuwarta kan matakin Dangote na ƙin barin ma'aikatan matatarsa su shiga cikin ƙungiyar.

Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa yarjejeniyar da suka cimma da matatar ɗangote da sauran rukunonin kamfanin ita ce za a bai wa direbobin manyan motocin dakonsu damar shiga ƙungiyar bisa raɗin kansu, matakin da matatar ɗangoten ke adawa da shi.

Yajin aikin ya haifar da fargabar samun ƙarancin man fetur a ƙasar.

An shawo kan ƙungiyar ne bayan tattaunawar sulhu ta kwana biyu da ministan ƙwadagon ƙasar ya jagoranta tare da haɗin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

Babban layin wutar lantarki na Najeriya ya sake lalacewa

Layin lantarki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Larabar 10 ga watan Satumbar 2025 ne babban layin wutar lantarkin Najeriya sake lalacewa a karo na farko a shekarar.

Duk da cewa babu cikakkun alƙaluma dangane da yawan lokacin da babban layin wutar lantarkin na Najeriya ya lalace, bayanai sun nuna cewa ya lalace sau fiye da 100 a tsawon shekaru 10 sannan sau 12 a shekarar 2024.

Bayanin da kamfanin wutar lantarki na Abuja, AEDC ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa wutar ta faɗi daga megawatts kusan 3000 a ƙasar zuwa megawatts 1.5 a ranar Larabar.

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/X

A ranar Alhamis gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da suka shafi auren jinsi da dangoginsa.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar ranar Laraba.

Cikin ƙunshin ƙudurorin da majalisar zartaswar ta aike wa majalisar dokokin - wanda kwamishinan ƙasa da safiyo, Abduljabbar Mohammed Umar ya sanya wa hannu, ta buƙaci da majalisar ta amince da dokar da za ta haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi a a faɗin jihar.

Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke amfani da shari'ar addinin musulunci - wadda a dokokinta suka haramta auren jinsi, tare da tanadar hukunci mai tsanani ga wanda ya aikata.