'Yan Real Madrid da aka gayyata tawagoginsu buga wasa

Asalin hoton, Getty Images
A karshen makon nan ba wasannin Lik da za a buga, sakamakon lokaci ne da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ware don buga karawa tsakanin tawagogin duniya.
A irin wannan lokacin ake buga wasannin neman shiga wata babbar gasa ko kuma fafatawar sada zumunta da sauransu.
Hakan ya sa tawagogi da yawa suka gayyaci 'yan kwallon Real Madrid domin su wakilci kasashensu.
Cikin 'yan wasan Real Madrid da aka gayyata sun hada da Carvajal da Asensio (Spain), Courtois da Hazard (Belgium), Mendy da Camavinga da kuma Thouameni (France)
Sauran sun hada da Modrić (Croatia) Alaba (Austria) Rüdiger (Germany), Lunin (Ukraine), Militão da Vini Jr. da kuma Rodrygo (Brazil) da Valverde (Uruguay).
Jerin wasannin da 'yan Real Madrid za su buga wa kasashensu:

Asalin hoton, EPA
Spain da Switzerland (Asabar, 24 ga watan Satumba)
Portugal da Sapin (Talata, 27 ga watan Satumba)
Carvajal da Asensio za su buga wa Sifaniya karawa biyu a Nations League.
Belgium da Wales (Alhamis 22 ga watan Satumba)
Netherlands da Belgium (Lahadi 25 ga watan Satumba)
Belgium ta gayyaci Courtois da Hazard, domin su yi mata wasa biyu a Nations.
France da Austria (Alhamis 22 ga watan Satumba)
Denmark da France (Lahadi 25 ga watan Satumba)
Tawagar Faransa za ta yi karawa biyu a Nations League, shi ya sa ta kira Mendy da Camavinga da kuma Tchouameni.

Asalin hoton, Getty Images
Croatia da Denmark (Alhamis 22 ga watan Satumba)
Austria da Croatia (Lahadi 25 ga watan Satumba)
Kyaftin Modrić zai buga wa Croatia wasa biyu a Nations League.
France da Austria (Alhamis 22 ga watan Satumba)
Austria da Croatia (Lahadi 25 ga watan Satumba)
Austria ta gayyaci Alaba fdomin ya yi mata wasa biyu a Nations League.
Germany da Hungary (Juma'a 23 ga watan Satumba)
England da Germany (Litinin 26 ga watan Satumba)
Rüdiger zai wakilci Jamus wasa biyu da za ta fafata a Nations League.

Asalin hoton, Getty Images
Scotland da Ukraine (Laraba 21 ga watan Satumba)
Armenia da Ukraine (Asabar 24 ga watan Satumba)
Ukraine da Scotland (Talata 27 ga watan Satumba)
Ukraine za ta buga wasa a Nations League, shi ya sa ta kira Lunin’.
Brazil da Ghana (Juma'a 23 ga watan Satumba)
Brazil da Tunisia (Talata 27 ga watan Satumba)
Brazil za ta buga wasan sada zumunta biyu, shi ya sa ta gayyaci Militão da Vini Jr. da kuma Rodrygo.
Uruguay da Iran (Juma'a 23 ga watan Satumba)
Canada da Uruguay (Talata 27 ga watan Satumba)
Uruguay ta kira Valverde , domin ya yi mata wasa biyu na sada zumunta.











