Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta koma kan ganiya - Pep Guardiola
Pep Guardiola ya ce Manchester United na kan hanyar komawa kan ganiya da za a yi rububin kaka gida a matakin farko a kan teburin Premier a bana.
Rabon da United ta lashe Premier League tun 2013, kuma kofi na karshe da ta dauka a fannin tamaula tun 2017.
Sai dai kawo yanzu ta yi wasa bakwai a jere ba a doke ta ba, tun bayan rashin nasara a gidan Manchester City da ci 6-3 a gasar Premier karkashin Erik ten Hag.
''Ina ji a jiki na cewar United na kan hanyar komawa kan ganiya,'' in ji Guardiola.
''A karshe dai United ta koma kan ganiya - na kalli abin da ya faru ranar Alhamis da ta doke FC Sheriff 3-0 da kwazon da ta sa a gidan Chelsea a minti 45 na farko da suka tashi 1-1 a karshen mako.
''Ina sha'awar abin da nake gani a United a yanzu haka. Akwai kungiyoyi da dama da suke sa kaimi kamar yadda United ke yi a kakar nan.
Dalilin da ya sa kenan ya kamata ka saka kwazo, domin zuwa Champions League da kuma lashe Premier.''
United tana ta shida a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila a bana da maki 20, bayan da ta ci wasa shida da canjaras biyu aka doke ta karo uku.
Haka kuma kungiyar ta Old Trafford ta ci kwallo 16 aka zura mata 16 a raga kawo yanzu bayan wasan mako na 13.
Kociyan Manchester City, ya kara da cewar Newcastle ma ta shigo cikin kungiyoyin da za a dama da ita cikin 'yan hudun farko a teburi ko tta lashe kofin bana.
''Newcastle ma ta nuna kanta,'' kamar yadda Guardiola ya sanar, wanda City ke fatan dauka Premier League na uku a jere.
''Na kalli wasansu da Tottenham. Masu tsaron bayansu sun hana Kane da Son sakat, babu matsala ko kadan.''
Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League mai maki 28 da tazarar maki biyu ttsakaninta da Manchester City maii biye da ita.
Wasannin Premier League na mako na 12:
Asabar 29 ga watan Oktoba
- Leicester City da Manchester City
- Newcastle United da Aston Villa
- Crystal Palace da Southampton
- Bournemouth da Tottenham
- Brighton da Chelsea
- Brentford da Wolverhampton
- Fulham da Everton Match details
- Liverpool da Leeds United