Roma na son Casmero, Napoli da Juventus na son Hojlund

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Roma na son dan wasan tsakiya na Brazil mai taka leda a Manchester United Casemiro, 32, a matsayin aro kafin kakar wasa, sai dai matakin ya danganta ne idan an saida dan wasan Argentina Leandro Paredes, 30. (Mail)

Napoli da Juventus na sa ido kan dan wasan gaba na Denmark mai taka leda a Manchester United Rasmus Hojlund, 21, sai dai har yanzu dan wasan ya gagara birge sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar wato Ruben Amorim. (Talksport)

Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya na fatan shirin dauko dan wasan gaba na Masar mai taka leda a Liverpool, wato Mohamed Salah, 32, a kakar wasan bayan soke kwantiragin dan wasan gaba na Brazil ato Neymar mai shekara 32. (Telegraph)

Wolves na fatan kokatrtawa kan dan wasan gaba na Brazil Matheus Cunha kafin wa'adin musayar 'yan wasa, ya yin da kungiyoyin Aston Villa, Arsenal da Nottingham Forest s ma ke son dan wasan mai shekara 25. (Football Insider)

Bayer Leverkusen ta daina sa ido kan dan wasan tsakiya na Manchester City, James McAtee, 22, ya yin da kulub din na Bundesliga ke son dauko dan wasan Argentina Emiliano Buendia, 28, daga Aston Villa. (Florian Plettenberg)

Lokaci na neman kurewa Manchester City kan dauko dan wasa Andrea Cambiaso, 24, a daidai lokacin da kungiyar da ya ke takawa leda ta Juventus za ta fadi matsayar karshe idan sun kammala wasa da Benfica a gasar Champions League a ranar Laraba. (Give Me Sport)

Manchester United na gab da dauko dan wasan Denmark mai taka leda a Lecce Patrick Dorgu, 20,kan kudi fam miliyan30m. (Sky Sports)

Liverpool za ta yi wa dan wasan tsakiya Stefan Bajcetic ajin 'yan kasa da shekara 21 kiranye, daga inda ya ke zaman bashi, inda za su tura dan wasan mai shekara 20 zuwa Las Palmas har zuwa karshn kakar wasa. (Atlantico Hoy - in Spanish)

Brighton ta shirya domin saida dan wasan Ireland Evan Ferguson, 20, kafin a rufe kasuwar saye da saida 'yan wasa a mako mai zuwa. (Athletic)

Bayer Leverkusen na tattaunawa da Brighton kan dan wasaFerguson. (Sky Sports)