Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Casemiro: Dan kwallon ya buga wa Real wasa na 250 a karawa da Inter
Ranar Laraba Real Madrid ta doke Inter Milan a Gasar Champions League a Spaniya, kuma karon farko da ta yi nasara a wasannin bana.
Real ta yi nasara ne da ci 3-2 ta kuma fara cin kwallo ta hannun Karim Benzema, sannan kyaftin Sergio Ramos ya ci ta biyu, kuma na 100 da ya zura a raga a Real Madrid.
Casemiro yana daga 'yan wasan da suka buga wa Real Madrid karawar, kuma wasa na 250 da ya buga wa kungiyar kenan.
Dan kasar Brazil wanda ke kaka ta Bakwai a kungiyar ta Real Madrid wacce aka yi nasara da shi a fafatawa 171.
Ya kuma lashe Champions League hudu da kofin Zakarun nahiyoyin duniya uku wato Club World Cup.
Haka kuma ya dauki UEFA Super Cups da kofin La Liga biyu da Copa del Rey da Spanish Super Cup biyu.
A wasa 250 da ya buga wa Real sun hada da 162 a La Liga da 55 a Champions League da 20 a Copa del Rey da shida a Club World Cup.
Sauran wasannin sun hada da karawa hudu a Spanish Super Cup da wasa uku UEFA Super Cup.
A kakar 2017/18 ce dan kwallon ya buga wasa da yawa har guda 48, a bana kuwa ya yi wa Real wasa 10 da cin kwallo daya a fafatawa da Borussia Mönchengladbach.
Kungiyar Barcelona a wasan El Clasico ita ce ya fuskanta da yawa har 15, sai dai karawa da Espanyol ita ce fafatawar da aka yi da shi aka samu nasara 10.
Wasannin Real Madrid biyar nan gaba da za ta fafata:
Lahadi 8 ga watan Nuwamba La Liga
- Valencia da Real Madrid
Asabar 21 ga watan Nuwamba La Liga
- Villarreal da Real Madrid
Laraba 25 ga watan Nuwamba Champions League
- Inter da Real Madrid
Lahadi 29 ga watan Nuwamba La Liga
- Real Madrid da Alaves
Talata 1 ga watan Disamba Champions League
- Shakhtar da Real Madrid
Casemiro, dan kwallon Brazil ya ci kwallo 24, inda 17 a La Liga da shida a Champions League da kuma daya a UEFA Super Cup.