Mourinho ba ya wariyar launin fata in ji Drogba

Asalin hoton, Getty Images
Didier Drogba ya ce tsohon kociyan Chelsea, Jose Mourinho ɗan kasar Portugal baya wariyar launin fata.
Galatasaray ta soki mai horar da Fenerbahce, Mourinho da yin kalaman wariya, bayan da suka tashi ba ci a Turkish Super Lig ranar Litinin.
Bayan tashi daga karawar ta hamayyar ƴan birnin Istanbul, Mourinho ya ce masu masaukin baƙi sai ''tsallen murna suke kamai birrai.''
Sai dai Drogba, wanda ya ci ƙwallo 20 a wasa 53 a Galatasaray a 2013/14 ya kare kalaman Mourinho, wanda ya horar da shi a Chelsea.
Kamar yadda Drodga ya sanar a shafinsa na X, ''Mun kwan da sanin yadda wasan hamayya yake, kuma na yi sa'a na san yadda karawar take.''
''Na ga kalaman da aka yi a baya kan Jose Mourinho. Ina son ku yadda da ni idan na ce muku na san Jose shekara 25 baya wariyar launin fata, kuma tarihin baya da na nan gaba zai tabbatar da hakan.''
''Ta yaya za a ce baba na ɗan wariyar launin fata ne, haba dai.
Mourinho tsohon kocin Chelsea da Manchester United da kuma Real Madrid ya karɓi aikin horar da Fenerbahce a Yunin 2024 bayan da ya bar Roma.
Tun kan wasa da Galatasaray, Mourinho ya caccaki alkalan wasan tamaula na Turkiya da cewar da wani daga ciki ne ya busa wasan da an ci karo da takaddama.
An gayyato raflin Slovenia, Slavko Vincic bayan da kungiyoyin suka amince a naɗa wani daga waje ya busa karawar.











