An yi wa ɗan wasan Barcelona ɗinki a fuskarsa

A

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kungiyar Barcelona ta ce ɗan wasan bayanta Pau Cubarsi yana nan ƙalau, bayan ƙinki 10 da aka yi masa domin rufe raunin da ya ji a fuskarsa.

Kocin ƙungiyar Hansi Fliks ya ce ɗan wasan Spain din mai shekara 17 an yi canjin shi ne a wasan da Barcelona ta doke Red Star Belgrade 5-2 a Gasar zakarun Turai a ranar Laraba.

Dan wsan ya ji rauni ne a wajen wata kwana da aka yi da suka haɗu da Uros Spajic.

Cubarsi wanda ya fara bugawa Barcelona wasa yana da shekara 16, sai da aka yi masa aiki a cikin filin wasa gabanin cire shi, bayan raunin da ya ji fuskarsa ta cika da jini.

Bayan gama wasan Flick ya ce "sai an yi masa ɗinki, amma yana nan ƙalau."

Daga baya Barcelona ta wallafa hoton ɗan wasan am rubuta "ina lafiya."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X