'Yan Bayern da ke jinya da ya hada da Musiala da Pavard

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Bayern Munich, Jamal Musiala na jinya, bayan raunin da ya ji a lokacin atisaye, kamar yadda kungiyar ta sanar.
Hakan ya hana dan kwallon zuwa atisaye tare da Benjamin Pavard, wanda ya kamu da rashin lafiya da kuma Raphael Guerreiro, wanda ke shirin komawa taka leda.
Ranar Lahadi 27 ga watan Agusta, Bayern Munich za ta karbi bakuncin, Augsburg, domin buga wasan mako na biyu a Bundesliga.
Bayern mai rike da Bundesliga ta je ta ci Werder Bremen 4-0 ranar 18 ga watan Agusta a wasan farko da fara kakar bana,
Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Leroy Sane da ya zura biyu a raga da Harry Kane da Mathys Tel, kowannensu ya ci guda-guda.
Wasannin mako na biyu da za a buga na Bundesliga:
Ranar Juma'a 25 ga watan Agusta
- RB Leipzig da Stuttgart
Ranar Asabar 26 ga watan Agusta
- VFL Bochum da Borussia Dortmund
- SC Freiburg da Werder Bremen
- 1. FC Koln da Wolfsburg
- SV Darmstadt 98 da Union Berlin
- FC Heidenheim da Hoffenheim
- Borussia Monchengladbach da Bayer 04 Leverkusen
Ranar Lahadi 27 ga watan Agusta
- FSV Mainz 05 da Eintracht Frankfurt
- FC Bayern Munich da Augsburg









