Shugaban kasar da ba ya so mataimakinsa ya gaje shi

Asalin hoton, AFP
Kasar Kenya, daya daga cikin kasashen Afirka mafiya karfin tattalin arziki, tana shirin zaben sabon shugaban kasa a ranar 9 ga watan Augusta a daidai lokacin da ake samun karuwar tsadar rayuwa da mummunan fari lamarin da zai kasance babban kalubale ga duk wanda ya yi nasarar zamantowa shugaban kasar.
Shugaba Uhuru Kenyatta na goyon bayan mutum da ke yin adawa da mataimakinsa domin ganin ya gaje shi.
Dukkanin zabukan kasar a baya sun janyo ce-ce-ku-ce - kama daga zargin tafka magudi da barkewar tarzoma da sauransu.
A zaben da za a yi a bana, ‘yan Kenya na fatan zabukan su zamanto na daban.
Su waye ne ‘yan takarar?
Raila Odinga, wanda ya sha kaye har sau hudu a neman kujerar shugaban kasa, ya sake fitowa a yanzu domin gwada sa’arsa.
Tsohon firaministan, mai shekara 77, ya yi suna a kasar wajen gudanar da yakin neman zabe.
Babban abokin hamayyarsa, shi ne mataimakin shugaban kasar William Ruto, mai shekara 55.
Ya nuna wa Mista Odinga cewa za su yi karon-batta a zaben musamma ma ganin irin dandazon jama’a da ya tara a yakin neman zabensa.

Asalin hoton, AFP
Akwai wasu ‘yan takara biyu na kananan jam'iyyu da za a fafata da su a zaben.
George Wajackoyah, na daya daga cikin ‘yan takarar kananan jam'iyyu, kuma ya dauki hankalin mutane kan batun da ya yi cewa idan ya samui nasara zai amince wajen noman tabar wiwi a kasar da kuma fitar da dafin macizai zuwa kasashen waje.
Shi kuma David Mwaure Wahaiga na gudanar da yakin neman zabe ne a kan batun yaki da cin hanci da rashawa.
Me ya sa shugaban kasar ba ya goyon bayan mataimakinsa?
Abubuwa sun yi kamari a siyasar kasar Kenya. Mista Odinga ya kasance babban abokin hamayyar Shugaba Uhuru Kenyatta a baya.
Hamayyar da ke tsakaninsu ta faro ne shekaru 60 da suka wuce, lokacin da mahaifansu, wadanda jagororin neman ‘yanci ne a kasar, suka juyawa juna baya.
Sai dai a wani abin al’ajabi, Kenyatta da Odinga sun gaisa da juna a lokacin da suka hadu a 2018, inda Mista Kenyatta ya nuna goyon bayansa ga Mista Odinga.
Hakan bai yi wa mataimakinsa Mista Ruto dadi ba, lamarin da ya sanya dangantaka tsakaninsu ta yi tsami.
Mene ne babban batun da ake yakin neman zabe a kai?
Mataimakin shugaban kasar ya mayar da hankali a yakin neman zabensa kan batun farfado da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare.
A zabukan baya, batutuwan cin hanci da rashawa da kuma yin adalci su suka mamaye yakin neman zabe, amma a yanzu mutane na duba batun wanda ya kyautata tattalin arzikin kasar.
Mista Ruto ya taso cikin iyalan da ba su da wadata, amma a yanzu yana da arziki, kuma hakan ne ya sa ya bayyana kansa a matsayin jagoran talakawa.
A wannan kasar mai dimbin matasa, ya mayar da hankalinsa wajen ganin ya kawo tsare-tsare da za su samar wa matasa aikin yi - a 2018 ya kira kasar da suna ta "masu fafutuka" saboda fafutukar da 'yan kasar ke yi domin samun 'yan kudaden biyan bukatunsu.

Asalin hoton, AFP
A wani mataki da ba a saba gani ba, Mista Ruto ya raba wa mutane baro-baro a yakin neman zabensa.
Ya kuma bayyana fitowarsa takara a matsayin wani abu da zai kawo karshen mamaya da wasu tsirarun iyalai suka yi wa siyasar Kenya wadanda ya kira da iyalan Kenyatta da Odinga.
Mista Odinga dai, ya yi alkawarin ci gaba a kan manufofin da shugaba mai barin gado yake a kai da kuma kyautata rayuwar ‘yan Kenya ta hanyar ba su shilling 6,000 a kowane wata, muddin aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Ya kuma yi alkawarin gyara bangaren kiwon lafiyar kasar a cikin wani shiri da ya yi wa lakabi da " Baba Care’’, wanda hakan ke kara wa mutane ganinsa a matsayin uba a kasa mai mutum fiye da miliyan 56.
Shin akwai batun kabilanci a wannan zabe?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A Kenya, ana nuna kabilanci a zaben da ake yi a shekarun baya, kuma hakan ya janyo barkewar rikici a wasu lokuta, inda ake far wa mutane da kuma kashe su kan cewa sun fito daga wata kabila.
An samu barkewar tarzoma ta tsawon makonni a zaben shugaban kasar na 2007 mai cike da rudani, inda mutum 1,200 suka mutu sannan sama da 500,000 suka tsere daga gidajensu.
Tun bayan nan, ‘yan siyasa sun yi ta nanata muhimmancin gudanar da zabuka cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sai dai batun kabilanci na nan har yanzu.
Mista Odinga ya fito daga kabilar Luo yayin da Mista Ruto kuma dan kabilar Kalenjin ne, kuma dukkaninsu, za su dogara ne da kuri’un manyan kabilu domin samun nasara.
Sai dai a wani yunkuri na ganin sun sami nasara, dukkansu sun zabi wadanda za su yi musu mataimaka ne daga wata babbar kabila a kasar – Kikuyu.
Shi kuma Mista Odinga, ya zabi Martha Karua, inda ta zamo mace ta farko da za ta yi takara a wata babbar jam’iyyar kasar.
Ana nuna damuwa cewa za a iya samun barkewar rikicin kabilanci a wasu sassan kasar, inda wasu mutane ke komawa yankuna da kabilunsu suka fi rinjaye domin kauce wa fadawa cikin tarzoma.
Sai dai duba da abin da ya faru a zaben 2007, hukumomi na daukar matakai wajen ganin abubuwa sun tafi cikin tsanaki da kwanciyar hankali.
Shin za a yi zabukan cikin gaskiya?
Hankalin mutane kasar ta Kenya ya koma kan hukumar zaben kasar wajen ganin ko ta yi gyara a kan matsaloli da aka fuskanta wadanda kuma hakan ya janyo soke ainihin sakamakon zaben 2017 da sake gudanar da daukacin zaben.
Abin da ya janyo faruwar hakan shi ne matsala da aka samu da na’urar aikewa da sakamakon zabe daga rumfunan zabe, inda na’urar ta daina aiki a wasu wurare.
Lauyoyin ‘yan adawa da ke wakiltar Mista Odinga sun yi zargin cewa hakan ne ya janyo magudi a zaben.
Sai dai, a yanzu hukumomi sun ce sun dauki matakai wajen tabbatar da ganin shirin aikewa da sakamakon zaben ya tafi yadda ya kamata.
Bukatar samun sakamakon zaben a kan lokaci za ta dogara ne kan yadda na’urar za ta yi aiki, amma zuwa ranar 9 ga watan Augusta, wakilan ‘yan takara za su sanya ido kan kowane sakamakon zabe domin tabbatar da ba a yi musu magudi ba.
Za a gudanar da zabe a wasu kujeru ne?
A ranar zaben, ‘yan Kenya za su kuma kada kuri’a a kan wasu mukamai.
Bayan zaben shugaban kasa, ‘yan kasar za su zabi ‘yan majalisa da sanatoci da gwamnonin larduna da kuma sauran ‘yan majalisar dokoki na lardi.
Mata kuma na da karin kuri’a da za su kada domin zabar daya daga cikin mata wakilai 47 da za su yi wakilci a majalisar tarayya.
Yaya zaben zai gudana?
Za a bude rumfunan zabe sa’o’i 12 daga karfe 6:00 na safe agogon kasar. Duk wanda ya shiga layi kafin a rufe, za a bar shi ya kada kuri’a.
Da zarar an rufe kuma, jami’ai za su fara kirga kuri’u a kowace rumfar zabe.
Ba a dai san yaushe za a sanar da sakamakon zaben shugaban kasar ba, sai dai hukumar zaben kasar tana da wa’adin kwana bakwai na kirga illahirin kuri’un da aka kada.
Kafin dan takara ya samu nasara, sai ya sami sama da rabin kuri’un da aka kada a fadin kasar da kuma akalla kashi 25 na kuri’un da aka kada a lardunan rabin kasar.
Idan dan takara bai samu abin da ake bukata ba, za a shiga zagaye na biyu na zaben tsakanin manyan ‘yan takara biyu da ke sahun gaba.







