Abin da ya sa tasirin ƙabilanci a zaɓen Kenya ke raguwa

Kenya

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Yayin da ake shirin gudanar da babban zabe a kasar Kenya a ranar 9 ga watan Agusta, wakilin BBC Dickens Olewe ya rubuta cewa rarrabuwar kawuna sakamakon kabilanci ta dade tana durkusar da siyasar kasar ko da yake akwai alamun hakan na iya canzawa.

A ranar 20 ga Janairun 1994 da safe, na shiga cikin aji don bugar cikin ɗalibai.

Ba zan iya tuna abin da aka faɗa ba amma daya daga cikinsu ya zauna a ƙwaƙwalwata.

"Ubangijinku ya rasu," wani ɗalibi ya faɗi da ƙarfi.

Jaramogi Oginga Odinga, mataimakin shugaban kasar Kenya na farko wanda daga baya ya zama mutumin da ake girmamawa ya rasu.

Duk da cewa muna makarantar firamare ne, amma mun iya fahimtar yadda siyasar ƙabilanci take a ƙasarmu, don haka wannan dalibi ya fahimci irin babbar asarar siyasa da mutuwarsa ta yi wa al'ummar Luo.

Wasu malamai na sukar ra’ayin irin wadannan yara na nuna kabilanci hatta a azuzuwa.

Abu ne da ya riga ya zama jiki har ma ba a kallonsa  a matsayin matsala, amma a wasu lokutan yana da illa.

Irin haka ta sake faruwa da ni shekaru takwas daga bisani, inda wata yarinya ’yar shekara huɗu ta zo wurina a rana ta farko bayan fara aiki da wata ƙungiyar agaji da ke tallafa wa iyalai matalauta a Nairobi, ta tambaye ni cikin harshen Swahili, "Kai wanne kabila ne?’’

Ba ta ji daɗin amsar da na ba ta ba, musamman don daga baya na fahimci cewa ƙabilata ta kasance cikin muhawara mai tsanani da takwarorinta, mai yiwuwa sha'awarsu ta samo asali ne daga zance na siyasa na lokacin.

Ƙuruciya na da ban sha’awa, sai dai ban ji dadin abin da ya faru ba.

Darussan zamantakewa sun koya mini jure irin wadannan tambayoyin, sai dai na jima ina tunanin yadda za ta kalli amsa ta.

Siyasar Kenya cike take da muhawar kabilanci, sai dai ta fi ƙamari a tsakanin manyan ƙabilun.

Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yan siyasa kan yi amfani da wani abu da ya jima yana damun mutane da ke a alaƙa da al’ada da bambance-bambancenta don tayar da tarzoma ta yadda za su ci zabe.

Wannan dabarar ta tsufa a yanzu, kuma ana ci gaba da fama da mummunan sakamakonta a duka fadin duniya.

A Kenya, an yi wani lokaci da zama dan wata ƙabila na bayar da wasu damarmaki saboda wasu ba su da gata, wani lokacin ita ce kawai cancantar da ake yin la'akari da ita wajen neman aiki, da jefa ƙuri'a a zaɓe, ko ma a sami tagomashi na yau da kullum daga wani mai iko.

An yi hakan ne don wulakanta wasu da ɓata masu rai, lamarin da ke haifar da wariya ga wadanda ba ƴan ƙabilar ba, sannan ya ƙarawa ƴan ƙabilar iko da kuma ƙarfi.

Kenya ta gamu da munanan tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci bayan zaben shekarar 2007 mai cike da ce-ce-ku-ce, lokacin da aka kashe fiye da mutane 1,500, wasu daruruwan kuma suka jikkata, sannan wasu 600,000 suka tsere daga gidajensu.

A iya cewa lokacin tashin hankalin ne ya zama mafi zubar da mutuncin ƙasar tun bayan samun 'yancin kai.

Ƙasar da ake kallo a matsayin mai cike da zaman lafiya ta juya akalarta, har yanzu kuma tasirin hakan na ci gaba da shafarta.

Kenya

Asalin hoton, Getty Images

A yayin wannan zabe, wasu iyalai na shirin yin kaura na wani dan lokaci zuwa yankunan da kabilarsu ta fi yawa saboda gudun tashin fitina.

Sam Kona, Kwamishina a Hukumar Hadin Kan Kasa NCIC, ya shaida wa manema labarai cewa, "Kenya tana da tarihin bakin jini na korafe-korafen da ba a warware ba, da suka kai shekaru 50, da kan haifar da tashin hankali, kuma 'yan siyasa sun kware wajen haifar da tsoro tsakanin al'ummomi."

Ya kara da cewa, “Mutane sun makance da cewa wannan takara ce kawai a tsakanin masu fada a ji, kuma da zarar an gama, manyan za su hadu ko sun ci nasara ko ba su yi nasara ba.

Mista Kona ya ce tashe-tashen hankula a tsakanin al’umomin kananan hukumomin shida da NCIC ta yi wa lakabi da cewa za su iya yin zafi a zabe mai zuwa ne saboda “rashin damar yin sulhu”.

Ya yi nuni da cewa, Kenya ta amince da sabon kundin tsarin mulki a shekarar 2010, inda ta samar da kananan hukumomi 47  masu gwamnoninsu, don kawo karshen tunanin rikicin zabe.

Ya yi alkawarin cewa za a yi wa dukkan kananan hukumomi adalci, kuma za su samu kaso mai tsoka na kasafin kudin kasa don tsara nasu ci gaba.

"Abin takaici har yanzu yawancin 'yan Kenya na kallon shugabanci a matsayin babban tushen iko, lamarin da ke haifar da tashin hankali," in ji Mista Kona, yana mai karawa da cewa NCIC ta kara kaimi wajen samar da zaman lafiya a wuraren da za a iya ta da zaune tsaye.

A shekara ta 2005 ne masanin harkokin mulki John Githongo ya tsere daga kasar saboda wasu 'yan kabilarsa ta Kikuyu sun dauke shi a matsayin mayaudari bayan da ya fallasa wata badakalar cin hanci da rashawa a gwamnatin Shugaba Mwai Kibaki ta wancan lokacin, dan kabilar Kikuyu.

Ya shaida wa BBC cewa gangamin kabilanci bai cika fitowa fili ba a wannan yakin neman zabe, saboda mataimakin shugaban kasar William Ruto ya mayar da takarar kama tsakanin dangin manya da kuma masu fafutuka.

Ya caccaki babban abokin hamayyarsa, Raila Odinga, wani gogaggen dan siyasar adawa kuma dan mataimakin shugaban kasar Kenya na farko, wanda yanzu ke kawance da shugaba Uhuru Kenyatta, dan shugaban kasar na farko.

Yana tallata kansa a matsayin zakaran gwajin dafin masu fadi tashi, da ke neman goyon bayan jama’a.

Mista Odinga ya soki wannan tsari nasa, da yake bayyanawa a matsayin wani yunkuri na raba kan al'ummar Kenya bisa tsarin inda suka fito, ya kuma mayar da hankali kan yakin neman zabensa kan sakon hadin kai.

Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai a wani gagarumin sauyi daga yakin neman zaben da aka yi a baya, ’yan takarar biyu na gaba-gaba sun fi mayar da hankali wajen musayar ra’ayi kan kasuwaci da tattalin arziki da kuma zamantakewa.

Wannan ba abin mamaki ba ne domin zaben ya zo ne a cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, da rashin aikin yi da kuma basuka mai yawa da ake bin kasar.

A wani babban mataki makonni kadan kafin zaben, gwamnatin Shugaba Kenyatta ta sanar da cewa za a ba da tallafin fulawar masara da ake amfani da ita wajen samar da abinci a kasar, domin rage farashinta.

Mista Ruto yana kallon hakan a matsayin wani yunkuri na karfafa damar Mista Odinga a zaben.

Mista Kenyatta yana goyon bayan Mista Odinga a zaben, duk da cewa Mista Ruto ne mataimakinsa.

Alama ce ta sauya yanayin ƙawance a tsakanin ƴan siyasar Kenya da ke da rinjayen ƙabilanci.

A shekara ta 2007 Mista Odinga da Mista Ruto sun hada kai da Mista Kibaki, wanda Mista Kenyatta ke marawa baya.

Wasu daga cikin tashe-tashen hankula mafi muni bayan zaben 2007 sun hada da ‘yan kabilar Kalenjin ta Ruto da ‘yan kabilar Kikuyu irin su Kenyatta, inda aka kashe mutane saboda kabilarsu.

Sai dai a 2013 da 2017 Kenyatta da Ruto sun hada karfi da karfe da Odinga, dan kabilar Luo, sai dai Kenyatta ya ƙi amincewa da Odinga.

Murithi Mutiga, daraktan tsare-tsare na Afirka a kungiyar International Crisis Group, ya ce "'yan Kenya sun gaji da duk wani kawancen da suka yi ta gani a tsakanin manyan mutane."

Mista Githongo ya ce yayin da rikicin kabilanci ke karuwa a lokacin zabe, "mutane na auren juna nan da nan duk da "

Ya kara da cewa "A tsakanin matasa ba a samu matsala sosai ba amma 'yan siyasa na yin gangami bisa kabilanci."