Arsenal ta fara kakar Premier ta bana da kafar dama

Asalin hoton, Getty images
Arsenal ta fara kakar Premier League ta bana da kafar dama, bayan da ta hada maki uku a kan Nottingham Forest.
Arsenal ta fara zura kwallo a raga ta Eddie Nketiah a minti na 26 da fara tamaula, sannan Bukayo Saka ya ci na biyu a minti na 32.
Haka suka je hutu Arsenal, wadda ta dauki Community Shield a bana tana da kwallo 2-0 a raga.
An fara wasan da lattin minti 30, bayan da aka samu matsala a bangaren tikiti da ta kai magoya baya da yawa ba su shiga fili ba a kan kari.
Sauran minti takwas a tashi daga karawar Taiwo Awoniyi, wanda ya shiga karawar daga baya ya zare daya daga biyun da aka zuwa wa Nottingham Forest.
Arsenal wadda ta yi ta biyu a bara a Premier League za ta ziyarci Crystal Palace ranar Litinin 21 ga watan Agusta a wasa na biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ita kuwa Nottingham Forsest za ta karbi bakuncin Sheffield United ranar Juma'a 18 ga watan Agusta.





