Ko kun san wasu tarihin da Ronaldo ke fatan kafawa a Euro 2024?

Cristaino Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasa na farko da ya halarci gasar cin kofin nahiyar Turai karo shida, wato Euro.

Dan wasan da ke taka leda a Al Nassr ta Saudi Arabia ya buga wasan da Portugal ta yi nasara a kan Jamhuriyar Czech 2-1 ranar Talata a Euro 2024 a Jamus.

Ya haura takwaransa na Portugal, Pepe da Luka Modric na Crotia da kowanne ya ziyarci Euro karo biyar.

Tun bayan da Ronaldo ya fara buga Euro, kowacce gasar yana cin kwallo a raga, wanda ke fatan yin haka a fafatawar da ake yi a Jamus, wato Euro 2024.

Ronaldo mai shekara 39 na sa zama mai shekaru da yawa da zai zura kwallo a raga, idan har ya ci a gasar da Jamus ke karbar bakunci da aka fara 14 ga watan Yuni.

Haka kuma tsohon dan wasan Real Madrid na sa ran yin kan-kan-kan da mai tsaron ragar Sifaniya, Iker Casillas a matakin kyaftin da ya daga Euro karo biyu.

Ronaldo kyaftin din tawagar Portugal ya lashe Euro 2016, shi kuwa Casillas tsohon golan Real Madrid ya dauki Euro 2008 da kuma Euro 2012 a matakin kyaftin.

Ronaldo tsohon dan kwallon Manchester United ya fara wakiltar Portugal a Euro 2004 da 2008 da 2012 da 2016 da 2020 da wadda ake a bana ta 2024.

Portugal, wadda ta fara kakar bana da kafar dama a rukuni na shida za ta buga wasa na biyu a cikin rukuni Turkiya ranar Asabar.

Turkiya ce ta daya a rukuni na shida, bayan da ta doke Georgia 3-1 ranar Talata a wasan farko a cikin rukunin.

Wadanda suka buga Euro karo biyar

  • Pepe (Portugal 2008, 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Luka Modrić (Croatia 2008, 2012, 2016, 2020, 2024)

Wadanda suka buga Euro karo hudu

Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images

  • Lothar Matthäus (West Germany/Germany 1980, 1984, 1988, 2000)
  • Peter Schmeichel (Denmark 1988, 1992, 1996, 2000)
  • Alessandro Del Piero (Italy 1996, 2000, 2004, 2008)
  • Edwin van der Sar (Netherlands 1996, 2000, 2004, 2008)
  • Lilian Thuram (France 1996, 2000, 2004, 2008)
  • Olof Mellberg (Sweden 2000, 2004, 2008, 2012)
  • Gianluigi Buffon (Italy 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Petr Čech (Czech Republic 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Zlatan Ibrahimović (Sweden 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Andreas Isaksson (Sweden 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Kim Källström (Sweden 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Jaroslav Plašil (Czech Republic 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Lukas Podolski (Germany 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Tomáš Rosický (Czech Republic 2000, 2004, 2012, 2016)
  • Bastian Schweinsteiger (Germany 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Darijo Srna (Croatia 2004, 2008, 2012, 2016)
  • Giorgio Chiellini (Italy 2008, 2012, 2016, 2020)
  • Sebastian Larsson (Sweden 2008, 2012, 2016, 2020)
  • João Moutinho (Portugal 2008, 2012, 2016, 2020)
  • Olivier Giroud (France 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Toni Kroos (Germany 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Manuel Neuer (Germany 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Thomas Müller (Germany 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Ivan Perišić (Croatia 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Wojciech Szczęsny (Poland 2012, 2016, 2020, 2024)
  • Andriy Yarmolenko (Ukraine 2012, 2016, 2020, 2024)