Chelsea ta koma cikin ƴan huɗun farko a teburin Premier League

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta doke Southampton 4-0 a wasan mako na 27 a Premier League ranar Talata a Stamford Bridge.

Nkunku ne ya fara cin ƙwallo a minti na 24, sai Pedro Neto ya zura na biyu a raga da kuma Colwill da ya ci na uku.

Haka suka yi hutu suka koma zagaye na biyu Chelsea tana cin 3-0, daga baya ne ta kara na huɗu ta hannun Marc Cucurella.

Da wannan sakamakon Chelsea ta koma ta huɗun teburin Premier da tazarar maki biyu tsakani da Manchester City ta biyar.

Ranar Laraba za a ci gaba da wasan Premier, inda Manchester City za ta karɓi bakuncin Newcastle United a karawar mako na 27.

Nottingham Forest ta ci gaba da zama ta karshen teburi da 20 da maki tara, sakamakon nasara biyu da canjaras uku aka doke ta wasa 22.

Kafin a fara wasan na ranar Talata, wasu mutum kimanin 100 sun yi zanga-zanga da ɗaga ƙyallen da yake ɗauke da sakon ''Todd Boehly ya bar ƙungiyar.