Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben 2023: Siffofin mutumin da ya kamata 'yan Najeriya su zaba a matsayin shugaban kasa
A ranar Larabar nan ne jadawalin hukumar zaben Najeriya ya bai wa masu takarar kujerar shugaban kasa da ta `yan majalisar dattawa da wakilai damar fara yakin neman zabe.
Sai dai ana fargabar cewa bambancin addini da kudi da kuma bangaranci za su mamaye yakin neman zaben, duk kuwa da cewa akwai tarin matsalolin da ke addabar jama`a; ciki har da matsin rayuwa da tabarbarewar tsaro da kuma ilimi.
Wannan rana tana da muhimmanci saboda za ta bai wa jam'iyyun siyasa da 'yan takararsu damar fitowa su yi yakin neman zabe gadan-gadan kuma a sarari sabanin yadda suke rabewa da sunan bude ofisoshin jam`iyya a wasu birane da wasu taruka a bayan fagge.
Jam`iyyun siyasa goma sha shida ne suka tsayar da masu takarar kujerar shugaban kasa daga cikin jam`iyyun siyasa goma sha takwas da hukumar zaben Najeriya ta yi musu rajista.
Za a dai fara yakin neman zaben ne a wani yanayi da ake fama da matsin rayuwa da tabarbarewar tsaro sakamakon hare-haren `yan bindiga da satar mutane don karbar kudin fansa.
Sai kuma tabarbarewar ilimi, kasancewar jami`o`in gwamnati da ke Najeriyar sun shafe fiye da rabin shekara a rufe sakamakon yajin aiki.
Kuma duk da wadannan tarin matsalolin, a wannan karon, masana na cewa da yiwuwar matsalar bambancin addini da bangaranci da kuma siyasar kudi su fi kowane lokaci mamayar yakin neman zaben.
Dr Kole Shetima, masanin siyasa kuma shi ne shugaban Gidauniyar Mc Arthur a Najeriya, na da irin wannan ra'ayi. "Tabbas ['yan takara] za su yi amfani da bangaranci da addini da kudi da sauransu. Ni dai a ganina idan aka ba talakawa kudi su karba amma su je su zabi wanda suke so."
A lokuta da dama a Najeriyar an sha ganin wasu `yan siyasa na raba kayan masarufi kamar shinkafa da taliya da sabulu ko gishiri da sukari, da kuma dan kudin da ba zai yanke wa mutum talauci ba, duka da da sunan sayen baki ko kuri`ar su.
Wannan ne ya sa ma masu zabe, kowa da irin abin da yake dakon masu yakin neman zaben da shi.
Sai dai Dr Kole Shetima ya bayyana cewa rashin akida a tsakanin `yan siyasa ya sanya suna sauya jam`iyya kamar riga, don haka babu laifi idan masu zabe suka ba da fifiko a kan dan takara.
Sai dai ya shawarci jama`a cewa kada su bari dadin baki da jerin alkawura su dauke musu hankali su tsaya su yi amfani da mizani wajen gwada nauyin kowane dan takara.
'Yan takara suna cewa za su yi kaza da kaza amma ba sa tsaywa su yi bayanai ta yaya za su yi. Mene ne bambancin abin da za su yi da abin da aka yi a baya. Ya kamata mutane su lura me ye ya yi wanda zai gwada mana cewa zai iya cika alkawarin da ya yi," in ji masanin siyasar.
Yanzu dai hukumar zabe ta sakam ma jam'iyyun siyasa da `yan takara linzami don fara yakin neman zabe, amma za a iya cewa lamarin ya zo a karkace ga musamman wasu daga cikin manyan jam'iyyun siyasar, sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye su don haka ne aka zuba musu ido a ga yadda za su fara wannan gudu na yada-kanin-wani.