Wane tasiri dalibai za su iya yi a zaben Najeriya na 2023?

An wallafa

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta fitar sun nuna cewa dalibai kusan miliyan tara ne suka yi rajistar katin zabe na 2023 a yayin da ta rufe rajista a ranar Litinin din da ta gabata.

Wannan ya kama kashi 28 cikin 100 ke nan na duka masu katin zabe miliyan 31 a fadin Najeriya.

Daliban sun yanki rajistar ne a yayin da kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasar, ASUU ta shiga wata na shida tana yajin aiki domin tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta biya musu bukatunsu.

Yajin aikin yana matukar ci wa dalibai tuwo a ƙwarya.

Don haka masana ke ganin adadin dabilan da suka yi rajistar katin zaben abin lura ne a yayin da ake tunkarar 2023.

Hasashen masana na nuna cewa matasa za su yi matukar tasiri a zaben Najeriya mai zuwa, kuma rahoton da INEC ya fitar ya goyi bayan haka.

Matasa masu shekaru 18 zuwa 34 su miliyan 18 ne ke da katin zabe, kuma sun ninka rukunin shekaru da ke binsu sau biyu wato shekaru 35-49 da katin zabe miliyan 8 da dubu dari 6.

Masana harkokin siyasa irin su Kabiru Sa'idu Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano, ya shaida wa BBC cewa daliban suna iya magance matsalolin da ke addabar fannin ilimi ta hnayar zaben mutumin da suke ganin zai yi musu maganin matsalolin.

Ya kara da cewa "ba karamin tasiri dalibai da matasa suke da shi ba a zaben Najeriya, kuma za su iya yanke hukunci su karkata zaben, sai dai ba su san suna da wannan karfi ba.”

"A zabukan baya, ba a ganin matasa a kan layin jefa kuri’a. Ba wai yin katin zaben ba ne kadai ba, dalibai da matasa su san za su iya amfani da katin zaben zabensu domin biyan bukatunsu," a cewar Kabiru Sufi.

A daya bangaren kuwa, ‘yan kasuwa, manoma da matan aure za su taka rawa a zabe mai zuwa ganin adadin wadanda suka yi rajistar katin zaben da miliyan 4.5, miliyan 2.8 da kuma miliyan 2.5.

Har yanzu maza ne ke kan gaba a masu kati da miliyan 16, amma mata sun yi hobbasa wajen daura damara da yin rajistar zabe su kusan miliyan 15.

Wannan adadi abin dubawa ne a zabe mai zuwa, lura da yadda matsalolin tattalin arziki suka shafi mata a wadannan shekarun.

Su ma masu larurar nakasa ba su yi kasa a gwiwa ba, sun fita su dubu dari 2 sun yi rajista kamar yadda hukumar INEC ta bayanna.