Arsenal ta koma matakinta na daya a teburin Premier League

Gabriel Martinelli

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta ci Liverpool 3-2 a wasan mako na 10 a Premier League ranar Lahadi a Emirates ta koma ta daya a teburin gasar.

Arsenal ce ta fara cin kwallo a kasa da dakika daya da fara wasa ta hannun Gabriel Martinelli.

Karon farko da Arsenal ta ci kwallo a karamin lokaci da take leda a Premier League a gida tun bayan Oktoban 2011 lokacin da Robin van Persie ya ci Sunderland a dakika 29 da fara wasa.

Haka kuma wannan ne karon farko da Arsenal ta ci Liverpool a kankanin lokaci da fara wasa a Premier League a tarihi.

Liverpool ta farke ta hannun sabon dan wasan da ta dauka a bana, Darwin Nunez a minti na 34.

Daf da za suje hutu ne, bayan karin lokaci Gunners ta kara na biyu ta hannun Bukayo Saka, hakan suka yi hutu Arsenal da ci 2-1.

Suna komawa zagaye na biyu ne Liverpool ta farke ta hannun Roberto Firmino, kuma na shida da ya zura a raga a bana a Premier League.

Daga baya Arsenal ta ci kwallo na uku ta hannun Saka a bugun fenariti, bayan da aka yi wa Gabriel Jesus keta.

Kwallo na 20 kenan da Saka ya zura a raga tun fara buga wasannin Premier, ya kuma zama matashi na biyu da ya ci 20 a Arsenal, bayan Nicolas Anelka wanda yake da shekara 20 da kwana 41, Saka yana da shekara 21 da kwana 34..

Gabriel Martinelli ya zama matashi na farko da ya ci kwallo ya kuma bayar aka ci Liverpool a Premier League mai shekara 21 da kwana 113,

Dan kasar Brazil yana da hannu a cin kwallo 10 a wasa 14 da ya buga a babbar gasar tamaula ta Ingila, wanda ya ci biyar ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.

Arsenal ta koma matakinta na daya da maki 24 da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Ita kuwa Liverpool ta hada maki 10 tana tana kuma ta 10 a teburin Premier League na kakar nan.