Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kai wa jami'an EFCC hari a Abuja da Imo
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ce an kai wa jami'anta masu sa ido kan amfani da kuɗi a wajen zaɓe hari a Abuja da Imo.
Hukumar ta ce wasu 'yan daba ne suka kai wa jami'an nata hari a kusa da fadar sarkin Bwari da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Wata sanarwa da EFCC ɗin ta wallafa a shafinta na twitter ta ce, harin ya biyo bayan kame wani mutum da hukumar ta yi, wanda ya ke tsara siyen ƙuri'a a yankin na Bwari.
Sanarwar ta ce tuni hukumar ta kama mutumin mai kimanin shekara 30, sannan ta ƙwace jerin sunayen wasu mutane da ya riga ya tura musu kuɗi asusunsu na banki.
A lokacin ne fusatattun matasan suka yi kukan kura suka yi kan jami'an na EFCC inda suka farfasa gilasan motocin hukumar.
Hukumar ta ce sun samu nasarar tarwatsa matasan ne bayan da jami'anta suka yi harbi sama, don gargaɗin 'yan daban.
A jihar Imo ma, hukumar ta ce an kai wa jami'anta hari da bindiga, inda aka harbe su daga wasu motoci biyu a mazaɓar makarantar firamare ta Mann.
EFCC ta ce maharan sun gudu ala tilas, bayan da jami'an hukumar suka mayar da martani.
Hukumar dai na zargin cewa maharan masu siyen ƙuri'a ne.