Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ci gaba da samun sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa
Bayanai na ci gaba da fitowa kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dattijai da na ƴan majalisar wakilai da aka gudanar ranar Asabar a Najeriya.
Duk da cewa kawo yanzu babu alkaluma da INEC ta fitar a hukumance na sakamakon zaben, sakamakon da ake bayyana wa a mazabu sun cika kafofin sa da zumunta.
BBC ba ta kai ga tantance sahihancin mafi yawncin sakamakon da ake bayyanawa ba.
Tun da misalin karfe 2:30 na yammaci ne aka fara samun sakamakon zaɓen daga rumfuna daban-daban a faɗin Najeriya.
Amma zai yi wuya alkaluman su yi ƙarin haske kan ɗan takarar da yake gaba musamman a zaɓen shugaban ƙasa.
Hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta ta ce an samu tashin hankali a wasu jihohi da suka hada Edo da Bayelsa da Borno da Legas da Kogi.
Hukumar ta ce za a sake zaɓuka a wasu mazaɓu a jihar Bayelsa ranar Lahadi.
A jawabin da Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi dazun nan, za a buɗe cibiyar tattara sakamakon zaɓe gobe Lahadi da ƙarfe 12 na rana.
INEC ta ce tana fatan samun sakamakon ƙarshe cikin ƙanƙanen lokaci, amma ba ta bayyana rana ba.
Dokokin Najeriya sun tanadi cewa dole ne sai ɗan takarar shugaban ƙasa ya samu kashi 25% na yawan ƙuri'un da aka kaɗa a jihohi 24 na Najeriya da Abuja, kafin a samu wanda ya lashe zaɓe.