Yadda ƴan majalisar dokokin Ghana suka ba hamata iska

Majalisar dokokin Ghana

Asalin hoton, DAILY GRAPHIC/FACEBOOK

Bayanan hoto, Ƴan majalisar ɓangaren adawa sun janyo hatsaniya tare da lalata tebura da kuma wasu abubuwa na zauren tantancewar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Hatsaniya ta ɓarke a majalisar dokokin Ghana yayin da ƴan majalisa suka bai wa hamata iska lokacin tantance sunayen ministoci da sabon shugaban ƙasar Johm Mahama ya aike wa majalisar a ranar Alhamis da daddare.

Lamarin ya janyo lalata abubuwa da suka haɗa da kujeru da kuma makurufo, inda ƴan majalisar ɓangaren waɗanda ke cikin kwamitin tantancewar suka yi adawa da buƙatar cigaba da tantance ministoci cikin dare har karfe 11 agogon ƙasar.

Wasu mambobin kwamitin sun nuna turjiya saboda ɗaukar sa'o'i ana tantance wani minista.

Kwamitin ya ce yana da mutum uku da zai tantance, amma bayan tantance mutum biyu, sun ɗauki tsawon sa'a biyar wajen tantance wanda ake son naɗa wa ministan sadarwa Samuel Nartey George - mutane da dama sun ce yanzu lokaci ne da ƴan majalisar adawa za su girbi abin da suka shuka.

Sun bayyana cewa ƴan majalisa marasa rinjaye da ke cikin kwamitin na son ministan ya ba da hakuri kan kalaman da ya yi a kan alkalin alkalan ƙasar da tsohon shugaban ƙasar Nana Akufo-Addo da kuma mataimakinsa.

Ministan sadarwa

Asalin hoton, PARLIAMENT OF GHANA/FACEBOOK

Bayanan hoto, Kwamitin tantancewar ya shafe tsawon sa'a biyar yana tantance wanda ake son naɗa wa ministan sadarwa

Sai dai ministan ya faɗa cewa yana kan bakarsa kan maganganun da ya faɗa a kan tsohuwar gwamnati na cewa masu cin hanci da rashawa ne - inda kuma suka goyi bayan haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba wanda aka fi sani da galamsey a ƙasar.

"Ni mutum ne mai tsari, ba na guduwa kan duk abin da yi imani da shi, don haka ina kan bakata kan abubuwan da na faɗa kan tsohon shugaban ƙasa da kuma sauran jami'an gwamnati." in ji Samuel George.

Bayan ɗaukar tsawon lokacikwamitin yana tantance minsitan sadarwan, sai daga baya ya yanke shawarar cewa zai tantance sauran ministoci biyun, abin da ƴan majalisar adawa suka ce ba su amince ba.

Daga nan suka ƙaure da hatsaniya cikin zauren majalisar, inda aka watsar da kujeru da makurufo da kuma sauran abubuwa, tare kuma da cewa ba za a ci gaba da aikin tantancewar ba.

Shugaban ƴan majalisar ɓangaren adawa Alexander Afenyo-Markin ya ce: "ƴan majalisar gwamnati sun yi tunanin cewa sun fi karfin mu, sai dai mun ki amincewa da buƙatarsu a daren nan, amma za mu cigaba da tantancewar gobe inda za mu yi muhimman tambayoyi. Babu abin da zai dakatar da mu. Akwai ɓangaren da akawun majalisar yake goyon baya."

Majalisar dokokin Ghana

Asalin hoton, DAILY GRAPHIC/FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaban ƴan majalisar ɓangaren adawa Alexander Afenyo-Markin ya ce ƴan majalisar gwamnati sun ci zalinsu

Mutane da dama sun zargi shugaban majalisar na ɓangaren adawa Alexander Afenyo Markin cewa yana ɗaukar tsawon lokaci wajen yi wa ministocin tambayoyi.

Haka ma, an ce rana guda kafin tantance ministan sadarwan, Afenyo-Martin ya faɗa wa wani gidan talabijin Citi tv cewa "a matsayin jam'iyya, mun yanke shawarar cewa za mu tantance ministocin uku, dole ne ɗaya daga cikinsu ya ba da hakuri kan yadda ya soki tsohon shugaban ƙasa Nana Akufo-Adda a baya.

"Za mu tantance tare da amincewa da guda biyu, sai dai idan su ma suka yanke shawara ko ƙasa amsa tambaya a gaban kwamiti," in ji Afenyo.

Majalisar dokokin Ghana

Asalin hoton, DAILY GRAPHIC/FACEBOOK

Bayanan hoto, Wasu ƴan majalisa lokacin da suke dambatawa a cikin majalisar

Bayan da ƴan majalisar suka lalata abubuwan da ke cikin zauren majalisar, sun ɗage zaman tantance sauran ministocin biyu da suka haɗa da ministan lafiya da kuma na harkokin waje zuwa yau Juma'a 31 ga watan Janairu.

Shugaban ɓangaren gwamnati a majalisar Mahama Ayarigah ya nuna takaicinsa kan hatsaniyar da ta faru a majalisar.

"Ba za mu iya cigaba da tantance ministocin ba a halin yanzu saboda an lalata komai - kujeru da abin magana da kuma sauransu.

Ya ƙara da cewa: "muna miƙa hakuri wajen jama'a. Abin takaici ne a ce ƙasar da ake tsarin dimokraɗiyya a samu afkuwar irin haka."

"Ina ƙara rokonku - dukkan ɓangarori sun amince cewa a cigaba da tantancewar ranar Juma'a inda za mu nemi wani ɗaki na daban don yin aikin," in ji Mahama.

Majalisar dokokin Ghana

Asalin hoton, CITI FM/CHANNEL ONE TV

Bayanan hoto, An lalata tebura da makurufo da kuma sauran abubuwa lokacin da hatsaniyar ta kaure

Mutane da dama sun soki ƴan majalisar kan abin da ya faru.

A watan Janairun 2021, ƴan majalisar ƙasar ta Ghana sun bai wa hamata iska lokacin zaɓen kakakin majalisar.

Lokacin ya kasance na farko da ƴan majalisa suka dambata a zauren majalisar, abin da ya janyo tura sojoji da ƴan sanda domin shiga lamarin.

Mutane dai sun ce abin da ƴan majalisar suka yi zubar da kimar ƙasar ne.

"Saboda kana ɗan majalisa hakan ba yana nufin cewa ba za a iya hukunta ka ba saboda lalata kayan gwamnati. Abin Alla-wadai ne," kamar yadda wani mai bincike kan harkokin siyasa Mussah Dankwah ya rubuta a kafofin sada zumunta.

Wani malamin sashen kimiyyar siyasa a Jami'ar Ghana, Farfesa Ransford Gyampo ya ce: "Ƴan Ghana na son ƴan sanda su kama tare da hukunta kowane ɗan majalisa da ya lalata kayan gwamnati."

Majalisar dokokin Ghana

Asalin hoton, CITI FM/CHANNEL ONE TV

Bayanan hoto, Shugaban ɓangaren gwamnati a majalisar Mahama Ayarigah ya nuna takaicinsa kan abin da ya faru